
PDP dan Arewa zata tsayar shugaban kasa a 2023>>Dr. Junaid Muhammad
Tsohon dan majalisar Najeriya, Dr. Junaid Mohammed ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta riga ta yanke shawarar dan Arewa zata tsayar takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Ya bayyana hakane a wani Rahoton Independent inda yace duk dan siyasar da yaga cewa jam'iyyar da yake ba zata bashi damar samun mukamin da yake so ba, yana iya canja sheka.
Ya bayyana cewa alamu sun nuna karara PDP dan Arewa zata tsayar takarar shugaban kasa a shekarar 2023. Yace kuma duk wanda APC zata tsayar takara zai sha wahala sosai wajan samun karbuwa.
Yayi kintacen cewa, za'a yi siyasar Kabilanci a zaben. Yace kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari bashi da kwarjinin da zai jagoranci jam'iyyar tasa zuwa ga nasara tunda ma ga sauran abubuwa nan da dama da ya kasa.
“A politica...