
Wasu ‘yan bindiga sun harbi wata maijuna biyu a ciki, Da har ta kai ga Jaririn ya rasa ransa
Wata Mata ta rasa juna biyun ta bayan da wasu 'yan bindiga su ka harbe ta a ciki
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko suwaye ba, sun yi sanadin mutuwar juna biyu wata mata bayan da su ka harbeta a ciki.
Lamarin dai ya faru ne a kasar Uganda, inda a ka bayyana matar mai suna Denize Kabugho mai shekaru 26 wacce lamarin ya rutsa da ita a dai-dai lokacin data fito daga gida domin siyayya.
Mijin matar Geoffrey Mumbere ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar 3 ga watan Oktoba, Inda ya shaidawa Manema labarai da cewa, 'yan bindigar dake kan babur sun harbe matarsa a ciki da misalin karfe 8.30 na daren ranar Talata lokacin da ta fito waje domin siyen sikari a wani shago da ke kusa.
A cewar Mijin matar wanda ya bayyana cewa, matar sa bai wuce saura mako guda ta haihu ba, amma sai dai kas...