fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Kabiru Ado Panshekara

Hukumar karbar korafe-korafe ta jihar kano ta kame shugaban karamar hukumar kumbotso bisa laifin rarraba kayan a gaji na cutar corona ba bisa ka’ida ba

Hukumar karbar korafe-korafe ta jihar kano ta kame shugaban karamar hukumar kumbotso bisa laifin rarraba kayan a gaji na cutar corona ba bisa ka’ida ba

Kiwon Lafiya
Hukumar da ke karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kame shugaban karamar hukumar kumboto Alhj Kabiru Ado Panshekara bisa laifin rarraba kayan a gaji ba bisa ka'ida ba. Shugaban hukumar  Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya tabbatar da kamun shugaban karamar hukumar. A cewar sa, Shugaban karamar hukumar ya sabawa dokar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shekara 2008 ( kamar yadda aka yiwa gyara) Hukumar ta ce an zargi Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso ne da rarraba kayayyakin jin kai ga jami’an tsaro wadanda suka hada da ‘Yan Sanda, DSS, Shige da fice da dai sauransu da kuma jami’an Hisbah; Tsarin da ya saba wa tanadin sashe na 22, 23 da 26 na Dokar Jama’a da Dokar Laifin Cin Hanci da Rashawa ta shekarar 2008 (kamar yadda aka yi wa gyara).