
Da Dumi-Dumi:Yanzu haka ana Daurin Auren diyar sanata Kabiru Marafa da sauran ‘yan Mata Marayu 13 da ya dauki nauyin aurensu a Kaduna
Sanata Kabiru Maraba na aurar da diyarsa, A'isha a garin Kaduna. Yanzu haka da muke kawo muku wannan Rahoto ana kan daurin auren a Masallacin Almanar dake Unguwar Marafa ta jihar Kaduna.
Wani abin daukar hankali a daurin auren shine, Sanata Marafa yasa an taro masa 'yan mata Marayu 13 daga kananan hukumomi daban-daban dake jihar Zamfara inda ya musu komai na aure ya hada dana diyar tasa.