fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Kabo

Gwamnatin jihar Nasarawa ce ta bamu shawarar kai Sarki Sanusi garin Loko>>Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Nasarawa ce ta bamu shawarar kai Sarki Sanusi garin Loko>>Gwamnatin Kano

Siyasa
Kwaminishinan sadarwa na jihar Kano,Muhammad Garba yayi karin bayani kan kai Sarki Muhammad Sanusi II da gwamnatin jihar ta sauke garin Loko.   Yace Gwamnan jihar Nasarawa ne ya bayar da shawarar kai Sarki Sanusi garin Loko domin kamin sauke Sarki Sanusi, gwamna Ganduje yayi tunanin inda za'a kai sarkin.   Sai ya tuntubi Gwamnan jihar Nasarawa ya kuma bada shawararshi kan inda za'a kai Sarki Sanusi.   Yayi wannan bayanine a shirin Madubi dake Vision FM jihar Kaduna.   Ya kara da cewa, basu da niyyar wulakanta sarki amma daga baya da aka gano cewa garin da aka kaishi bashi da abubuwan more rayuwa da sarkin ya saba dasu. Sai aka Canja masa gari.