fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Kadpoly

Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Kaduna(KADPOLY) Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Domin Sake Bude Makarantar

Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Kaduna(KADPOLY) Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Domin Sake Bude Makarantar

Uncategorized
Shugaban kwalejin kiminyya da fasaha ta Kaduna(Kadpoly), Farfesa Idris Bugaje a ranar Alhamis ya ce makarantar da ke karkashin jagorancin shi ta dauki dukkan matakan da suka wajaba tare da shiri gurin sake budewa ga daliban da zarar ta samu amincewar  Gwamnatin Tarayya. Farfesa Bugaje, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a harabar babbar kwalejin, ya ce makarantar ta samar da na’urar wanke hannu wanda ta kera da kanta kuma ta samu fasahar zamani mai iya auna zafin jiki. A cewar sa, “muna da na'urar Ultraviolet, UV sanitizer. Muna amfani da wannan tare da 210 nanometer. Wannan bandwidth na hasken ultraviolet bai da cutarwa ga idanu ko fata. Don haka lokacin da mutum ya wuce ta cikin wannan injin, kowane irin kwayar cuta a jikin ku zata mutu. ” ...