
Jihar Kaduna ta sallami karin mutum 20 wadanda suka warke daga cutar coronavirus/covid-19
Sanarwar sallamar ta zone daga bakin gwamnan jihar Malam Nasiru El Rufai inda ya bayyana cewa bayan gwajin mutum 138 an samu mutum 4 wadanda suka harbu da cutar Wanda suke a Arewacin kaduna sannan da Karin mutum daya daga Chikun.
Baya ga haka gwamnan jihar kaduna ya sassauta dokar kulle da ya sanya a jihar tun bayan rahotan bullar cutar coronavirus ne gwamnan jihar ya sanya dokar kulle, a kokarin da gwamnati keyi wajan dakile yaduwar cutar a jihar.