fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Kaduna covid19

Covid-19: El-Rufai ya tabbatar da samun karin mutum 16 masu cutar coronavirus a jihar Kaduna

Covid-19: El-Rufai ya tabbatar da samun karin mutum 16 masu cutar coronavirus a jihar Kaduna

Kiwon Lafiya
Gwamanan jihar Malam Nasiru El-Rufai ya tabbatar da samun karin mutum 16 a cikin mutum 252 da aka yiwa gwajin cutar coronavirus a jihar. A sakon da gwamnan ya wallafa ta cikin shafinsa dake kafar sadarwa na tuwita a daran juma'a. Ya ce an samu karin ne a Arewancin jihar Kaduna har mutum 11, sannan Makarfi mutum 1, sai  Giwa mutum 2, Sabon gari mutum 1, da kuma kudancin jihar Kaduna mutum 1. Haka zalika a daran jiya Najeriya ta tabbatar da samun karin mutum 684 wanda adadin masu cutar ya karu da kimanin mutum 23,298.
Covid-19: A kalla mutane 608 jihar kaduna ta tabbatar sun harbu da cutar coronavirus yayin da aka sallami mutum 308

Covid-19: A kalla mutane 608 jihar kaduna ta tabbatar sun harbu da cutar coronavirus yayin da aka sallami mutum 308

Kiwon Lafiya
A cigaba da bayyana yanayin da jahohi ke ciki game da cutar coronavirus a Najeriya, jihar kaduna na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya DA cutar ta mamaya. A rahoton da jihar ta fitar game da al'kaluman cutar a jihar ya nuna cewa, a kalla an samu adadin mutum 608 masu fama da cutar, haka zalika jihar ta sallami mutum 308 baya ga haka an samu mutuwar mutum 14. Haka zalika jahar ta bayyana adadin samfurorin data gwada inda ya kai a kalla 5446.
Covid-19: Jahar Kaduna ta sallami yaro mai watanni hudu da haihuwa bayan ya warke daga cutar coronavirus

Covid-19: Jahar Kaduna ta sallami yaro mai watanni hudu da haihuwa bayan ya warke daga cutar coronavirus

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da sanarwar cewa ta sallami jariri mai watanni hudu da haihuwa bayan an tabbatar da warkewarsa daga cutar COVID-19. A cikin sanarwar da Kwamishinan lafiya, Dokta Amina Mohammed Baloni ta yi a ranar Asabar, Gwamnatin jahar kaduna ta ce daga cikin adadin mutum 232 da aka ruwaito sun harbu da cutar a jahar an kuma yi nasarar sallamar adadin mutum 149 baya ga haka an samu rahoton mutuwar mutum bakawai. Haka zalika Kwamishinan ta yi gargadin cewa '' jihar ta gwada kusan samfurori 2000, amma akwai yiwuwar lambobin su kara karuwa yayin da ake cigaba da gudanar da gwaje-gwaje a wurare da dama. Jahar ta samu rahoton masu dauke da cutar a cikin mazabu 33 dake  kananan hukumomi tara na jihar da suka hada da Chikun, Giwa, Igabi, Kaduna ta arewa, Kaduna ta kudu, Ma...
Jahar Kaduna ta sallami karin mutum 5 bayan sun  warke daga cutar Coronavirus/covid-19

Jahar Kaduna ta sallami karin mutum 5 bayan sun warke daga cutar Coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Jihar kaduna dake arewacin Najeriya na daya daga cikin jahohin da aka samu bullar cutar coronavirus.   Jahar tai nasarar sallamar mutum 5 bayan sake samun karin adadin mutum 12 masu dauke da cutar a jihar inda suka hada da mutum 6 a kaduna ta Arewa, sai mutum 4 a kaduna ta kudu, hadi da mutum 1 Chikin da kuma 1 a Igabi.   Hakan nakun she ne ta cikin sanarwar da gwamnan jihar Malam Nasir El Rufa'I ya wallafa ta cikin shafinsa dake dandalin tuwita @elrufai.    
Jihar kaduna ta sallami al’majirai 11 bayan sun warke daga cutar corona

Jihar kaduna ta sallami al’majirai 11 bayan sun warke daga cutar corona

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kaduna, a ranar Talata ta sanar da cewa an sallami marassa lafiya guda 11 wadanda da Almajiri ne  cikin jihar inda aka tabbatar da samun murmurewar su daga cutar. Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, a wani sako ta shafinsa na Twitter, ya tabbatar da hakan yayin da yake sanar da cewa an sallami marassa lafiya 12 da ke cikin jihar.   Yanzu haka dai jihar Kaduna ta sallami mutum 27. An shawarci mazauna yankin su ci gaba da kiyaye ka'idodin nesanta juna dan dakile yaduwar cutar.   A halin yanzu, Gwamnatin Jiha ta tabbatar da samun mutum  guda 92 masu corona a cikin Jihar.  
Coronavirus ta shiga kauyukan jihar Kaduna>>El Rufai

Coronavirus ta shiga kauyukan jihar Kaduna>>El Rufai

Uncategorized
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna damuwa kan karuwar masu dauke da cutar korona a wasu kauyukan jihar.     A cewarsa mutanen da suka kamu da cutar a yankunan karkara, sun shiga shigar ce ta barauniyar hanya, kuma a yanzu haka ana yada cuta sosai a tsakanin al'umma.     Sanarwar da kakakinsa, Muyiwa Adekeye ya fitar, ta ce an samu masu dauke da cutar a kananan hukumomi bakwai na jihar ciki hadda - Giwa da Igabi da Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu da Makarfi da Soba da kuma Zariya.     Sanarwar ta kara da cewa mutum hudu da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar - NCDC ta ce na dauke da cutar korona, sun shiga jihar ne daga wasu jihohin kasar.     A ranar Juma'a gwamna El Rufai ya yi rangadi zuwa was...
Duk da bude gari a yau, jihar Kaduna ta rufe gabadayan kasuwannin jihar inda ta bude na wucin gadi

Duk da bude gari a yau, jihar Kaduna ta rufe gabadayan kasuwannin jihar inda ta bude na wucin gadi

Kasuwanci
Duk da vude gari a Yah, Asabar dan baiwa Mutane damar sayen kana Abinci, jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kulle kasuwannin jihar inda ta bude wasu kasuwannin wucin gadi wanda tace a nanne mutane zasu rika zuwa sayen kayan Abinci.   Gwamnatin ta yi amfani da Filayen makarantu dake unguwannin cikin jihar wajan bude wadannan kasuwanni na wucin gadi.   Ta bayyana cewa ta yi hakane dan saukakawa mutane ba sai sun tashi sun yi tafiya me nisa ba wajan neman abinda suke son saye.   Tace za'a baiwa kowane dan kasuwa runfar da zai sayar da kayansa sannan mae saye da me sayarwar duk zasu kasance suna amfani da takunkumin rufe hanci da baki.   Ta kara da cewa akwai jami'an tsaro da zasu kasance a wadannan kasuwannin wucin gadi dan tabbatar da ganin an bi ...
Gwamnan Kaduna ya bukaci hadimansa su bayar da tallafin Dubu Dari 5 kowannensu

Gwamnan Kaduna ya bukaci hadimansa su bayar da tallafin Dubu Dari 5 kowannensu

Kiwon Lafiya
A sanarwar da ya fitar ta tsawaita zaman gida dole dan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 a Kaduna, Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bukaci masu rike da mukaman siyasa, hadimansa a jihar da kowannensu ya bayar da tallafin Naira Dubu Dari 5.   Gwamnan ya kuma kara da cewa daga yanzu za'a rika cirewa masu rike da mukaman siyasar kaso 50 cikin 100 na albashinsu har sai maganar killacewar ta wuce.   Sanarwar wadda ta fito daga hannun me baiwa gwamnan shawara ta fannin sadarwa,Muyiwa Adekeye ta kara da cewa su kuma ma'aikata masu daukar Albashin sama sa Naira Dubu 67 za'a rika cire musu kaso 25 cikin 100 na Albashinsu.   Karin abinda sanarwar ta kunsa shine samar da kotun tafi da gidanka dan yankewa wanda suka karya dokar jihar hukunci nan take.
Ana fargabar wani mutum ya yada cutar Corona a jihar kaduna

Ana fargabar wani mutum ya yada cutar Corona a jihar kaduna

Kiwon Lafiya
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana fargabar cewa, a kwai wani mutun da ya kamu da cutar coronavirus a garin Mando, wanda ake zargin ya yada ta tsakanin al’umma, duba da cewa, bai jima da dawowa daga jihar Lagos ba a cikin motar haya. Kwamishiniyar Lafiyar Jihar, Dr. Amina Mohammed Baloni ce ta bayyana mutumin a matsayin mai aikin gadi kuma tuni aka killace shi a cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta jihar. An gane cewa, yana dauke da cutar ne bayan rashin lafiyarsa ya tsananta, yayin da Kwamishiniyar Lafiyar ke cewa, abu ne mai matukar wahala da sarkakiya, a iya bin diddigin mutanen da ya yi hulda da su musamman fasinjojin da suka shiga mota tare da shi tun daga jihar Lagos. Kazalika mara lafiyar ya yi jerin zirga-zirga a cikin jihar kaduna cikin motocin haya daban daban bayan ...