fbpx
Monday, October 26
Shadow

Tag: kaduna

Jihar Kaduna zata bi gida-gida dan zakulo wanda suka wawushe tallafin Coronavirus/COVID-19

Jihar Kaduna zata bi gida-gida dan zakulo wanda suka wawushe tallafin Coronavirus/COVID-19

Siyasa
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa zata bi gida-gida dan zakulo wanda suka wawushe tallafin Coronavirus/COVID-19 a kamasu.   Mataimakiyar gwamnan jihar wadda itace mukaddashiyar Gwamna, Dr. Hadiza Balarabe ce ta bayyana haka a wani jawabi da tawa mutanen jihar. Tace babu wani suna da za'a kira abinda mutanen da suka wawushe tallafin Coronavirus/COVID-19 suka yi banda sata. Tace sata ce kuma za'a bi sahunsu dan kamasu su fuskanci hukunci.   Tace sun bi sun tattauna da shuwagabannin yankuma kuma za'a kama hadda wadanda suka taimaka aka yi wannan aika-aika inda tace ba za'a bari wasu dake tunanin sun fi karfin doka su yi abinda suke so ba ana kallonsu.   Tayi gargadin cewa abinci da magunguna da aka dauka ma wasunsu sun lalace.   “There c
Masu garkuwa da mutane sun kashe soja me mukamin Kanal da suka kama a Kaduna duk da biyan kudin Fansa Miliyan 10

Masu garkuwa da mutane sun kashe soja me mukamin Kanal da suka kama a Kaduna duk da biyan kudin Fansa Miliyan 10

Siyasa
Masu garkuwa da mutane a Kaduna sun kashe soja me mukamin Kanal da suka kama a kwanakin baya duk da biyansu kudin fansa na Miliyan 10.   Yan bindigar sun kama SB Onifade a kusa da kamfanin Olam dake Kaduna ranar 27 ga watan Satumba inda kuma suka nemi kudin Fansa. Wata majiya ta gayawa Daily Nigerian cewa abokai sun hada Miliyan 10 aka bayar dan karbo sojan amma duk da haka masu garkuwar saida suka kasheshi.   Tuni dai tun a lokacin da ake maganar biyan kudin Fansa hukumar Sojin ta kaddamar da bincike dan gano sojan.
Hotuna:Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyara inda matasa suka fasa rumbun ajiyar magunguna na NAFDAC

Hotuna:Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyara inda matasa suka fasa rumbun ajiyar magunguna na NAFDAC

Siyasa
Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Balarabe kenan a wadannan hotunan inda ta kai ziyara rumbun ajiyar magunguna na hukumar kula da Abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC.   Gwanan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa wasu bata gari ne suka fasa rumbun ajiyar suka wawuce magungunan da suka lalace da wasu masu illa. Acting Governor @DrHadiza Balarabe is inspecting the places that were looted yesterday by criminal elements. First port of call is NAFDAC where expired and dangerous drugs, office equipment and doors were stolen.
Kayan Abinci da Magunguna da kuka wawushe na da guba kuma duk wanda yaci zai iya Mutuwa>>Jihar Kaduna ta yi gargadi

Kayan Abinci da Magunguna da kuka wawushe na da guba kuma duk wanda yaci zai iya Mutuwa>>Jihar Kaduna ta yi gargadi

Siyasa
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadin cewa duk wanda suka waushe abinci a Kakuri da Nariya su kiyaye dan abincin da magungunan da suka wawushe na da matsala.   Kwamishinan harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka inda yace rumbun magunguna da aka fasa na hukumar kula da abinci da magunguna na ta kasa, NAFDAC tace magungunan na da illa kuma duk wanda yayi amfani dasu na iya shiga hadatin kamuwa da mummunan rashin Lafiya ko ma mutuwa.   Yace hakanan kayan Abincin da aka wawushe suma akwai wanda aka sakawa kemikal na hana abincin lalacewa.   Yace dan haka mutane su yi hankali da inda suke sayen abincin da zasu ci sannan kuma idan sun san inda wanda suka wawushe abincin suka kaishi su yi magana.   “Persons who consume such drugs are at g
Kotu Ta Fara Sauraran Kalubalen Karar Da Aka Shigar Game Da Sarkin Zazzau

Kotu Ta Fara Sauraran Kalubalen Karar Da Aka Shigar Game Da Sarkin Zazzau

Siyasa
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zaune a Dogarawa Sabon Gari a karkashin Mai Shari’a Kabir Dabo ta fara sauraren karar da aka shigar a gabanta game da batun kalubalantar nadin da akawa Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau da gwamnan Kadun Nasir El-Rufai ya yi. An nada Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 bayan rasuwar tsohon sarki Shehu Idris. Aminiya a baya ta kawo rahoton kalubalantar nadin da daya daga cikin masu neman kujerar, Bashar Aminu ya yi. Aminu yana daga cikin manyan 'yan takara hudu da masu nada sarki suka zaba domin gwamnan ya nada. Ya samu mafi girman maki a cikin martaba ta masu nada sarkin. Amma an cire jerin kuma gwamnati ta ba da umarnin sabon zabi. Sabon jerin ya hada da Bamalli wanda daga karshe aka zaba. Aminu, a cikin kar
Bidiyo da Hotuna:Matasa Sun fito zanga-zanga a Kaduna

Bidiyo da Hotuna:Matasa Sun fito zanga-zanga a Kaduna

Tsaro
Matasa a jihar Kaduna sun fito zanga-zanga ta bukatar gwamnati ta dauki mataki kan matsalar tsaron da ake ciki a Arewa.   Matasan na amfani da maudu'in #SecureNorth inda suke rike da kwalaye dake nuna a kawo karshen Garkuwa da mutane, Fyade, a Kawo karshen zubae da Jini. https://twitter.com/jeebryl/status/1317362748041428995?s=19  
Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken cin zarafin ‘yansanda

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken cin zarafin ‘yansanda

Tsaro
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kafa kwamitin Binciken zargin cin zarafi da yansanda ke yi.   Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne ya bayyana haka inda yace mai shari'a, David Shiri Wyom ne zai jagoranci kwamitin.   Ya bayyana cewa akwai kuma kungiyoyin fafutukar al'umma dana matasa da za'a saka cikin kwamitin. https://twitter.com/GovKaduna/status/1317151185233739776?s=19 Malam Nasir @elrufai has approved the constitution of a judicial commission of inquiry into acts of brutality by police units in the state. The inquiry will be chaired by Hon. Justice David Shiri Wyom (rtd.), with representatives of civil society and youth groups as members.
Daliban jami’ar jihar Kaduna, Kasu 17 sun kamu da Coronavirus/COVID-19

Daliban jami’ar jihar Kaduna, Kasu 17 sun kamu da Coronavirus/COVID-19

Siyasa
Daga Jihar Kaduna, Rahotanni sun bayyana cewa daliban dake karatu a tsangayar koyan aikin Likita 17 ne suka kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.   Hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar ASUU na jami'ar, Comrade Tukur Abdulkadir inda yace ranar jarabawa da makarantar ta saka a matsayin Litinin me zuwa ba abune da zai yiyu ba. Yace sake bude makarantar kansa bayan kan ka'ida saboda gwamnatin Jihar Kaduna bata bada izinin haka ba, sannan kuma dalibai na mu'amala ba tare da yin nesa-nesa da juna ba ko kuma saka takunkumin rufe baki da hanci ba sannan dakunan kwanan daliban a cunkushe suke.   Ya bayyana cewa babu wani mataki na kariya daga cutar Coronavirus da jami'ar ta dauka.   Yace a baya cikin daliban tsangayar karatun aikin Likita 50 da aka kir...