Wednesday, June 3
Shadow

Tag: kaduna

An Cafke Mutum 165 a Kaduna Bisa Karya Dokar Zama a Gida

An Cafke Mutum 165 a Kaduna Bisa Karya Dokar Zama a Gida

Kiwon Lafiya
 A daidai lokacin da dokar hana zirga-zirga da tara jama'a a jihar Kaduna ke neman cika mako guda, rundunar 'yan-sandan jihar ta sanar da cafke mutum 165 bisa zargin karya dokar.     Mai magana da yawun rundunar 'yan-sandan ta Kaduna ASP Mohammed Jalige, wanda ya bayyana hakan, ya ce rundunar ta kama motoci da babura sama da 200.     Ya ce “an cafke mutum 165 da suka karya dokar zama a gida, kuma an kwace motoci da keke na pep a kalla 200.”     Ya kuma ce za a kama duk wanda ya kara karya dokar.     Tuni dai aka gurfanar da wasu daga cikin wadanda aka kama gaban kotu a jiya Litinin inji Lauyan gwamnati Dari Bayero.     Barr. Abdulbasid Suleman ne lauyan wadanda gwamnatin Kaduna ke zargi da karya
CORONAVIRUS: Kotu Ta Bada Belin Limamai Uku Da Suka Yi Sallar Juma’a A Jihar Kaduna Akan Naira Milyan Daya-Daya

CORONAVIRUS: Kotu Ta Bada Belin Limamai Uku Da Suka Yi Sallar Juma’a A Jihar Kaduna Akan Naira Milyan Daya-Daya

Kiwon Lafiya
Wata kotun majastare dake layin Ibrahin Taiwo, a Kaduna ta bada belin wasu Limamai 3 da suka gudanar da sallar Juma’a, duk da dokar hana zirga zirga da aka sanya a Kaduna a daidai lokacin.     An bada belin Muhammad Umar, wanda ake zargin ya karya dokar gwamnatin jihar na hana zirga zirga don dalkile yaduwa cutar corona virus.     An bada belin Umar ne tare da limamai Yusuf Hamza, Muhammad Ubale, da Auwal Shuaibu, wadanda ke zaune a unguwan Kanawa dake Kaduna, ana zargin su ne da laifin hada baki da bijirewa da dokar gwamnatin jahar.     Alkali Ibrahim Musa, ya kuma bayar da belin Hamza, Ubale da Shuaibu suma akan kudi Naira Miliyan 1 kowannne su.     Alkali musa ya kuma bukaci su samu wani sananne dake zaune a gar
Allah ya baka lafiya>>Ali Nuhu yawa Gwamna El-Rufai addu’a

Allah ya baka lafiya>>Ali Nuhu yawa Gwamna El-Rufai addu’a

Kiwon Lafiya
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu sarki ya jajantawa Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bisa cutar Coronavirus data kamashi.   A wani sako daya wallafa a shafinsa na sada zumunta,Ali Nuhu yace   Allah ya baka Lafiya mai girma Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Ya kuma kare dukkan al'umma da wannan cutar ta Covid-19. Jama'a a daure a Zauna a gida kuma a rage cudanya cikin taron mutane. Allah ya karemu baki daya. https://www.instagram.com/p/B-WgHQHh2-V/?igshid=1awepqcqb9j99   Gwamna El-Rufai na daga cikin manyan mutanen Arewa da cutar ta kama kuma tuni ya bayyana cewa ya killace kansa.
Gaskiya El-Rufai yayi abin yabo,  ‘yan Najeriya ku yi koyi dashi>>PDP

Gaskiya El-Rufai yayi abin yabo, ‘yan Najeriya ku yi koyi dashi>>PDP

Kiwon Lafiya
Wata Alamar siyasa ba da gababa da jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta nuna abin a yabane.   Jam'iyyar ta PDP reshen jihar Kaduna ta jinjinawa gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bisa fitowar da yayi ya bayyana cewa yana dauke da cutar Coronavirus/COVID-19,  ta bayyana wannan abu a matsayin abin bajinta.   Da take magana jiya, Lahadi ta bakin Sakaren jam'iyyar na jihar, Abraham Albera, PDP tace wannan zai karfafawa masu dauke da cutar a jihar suma su fito su bayyana ba tare da fargababa komkuma wanda ake zargin suna da ita, hakan zai sa su kai kansu a gwadasu.   PDP ta kara da cewa tana fatan Allah ya baiwa Gwamnan lafiya cikin gaggawa.   PDP ta kara da cewa tana jawo hankalin jama'ar jihar dasu yiwa dokar zama a gida biyayya dan dakile y
Ranar da abinci ya kare a gidan talaka, to Corona zai gane babu me tsoronsa>>Sanata Shehu Sani

Ranar da abinci ya kare a gidan talaka, to Corona zai gane babu me tsoronsa>>Sanata Shehu Sani

Kiwon Lafiya
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani yayi wata mata ta Shagube a shafinsa na sada zumunta.   Shehu Sani ya bayyana cewa, a ranar da abinci ya kare a gidan talaka, to Corona zai gane cewa babu me tsoronsa. Ya kara da cewa a yanzu dai ya ci gaba da cika baki.   https://twitter.com/ShehuSani/status/1244260558691536896?s=19   A jiyane dai gwamnan Kaduna, Malam  Nasiru Ahmad El-Rufai da basa ga maciji da Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ya kamu da cutar.   Kuma a yanzu haka mutanen Kaduna na tsare a Gida dan magance matsalar yaduwar cutar.
Nima yau zanje amin gwajin cutar Coronavirus/COVID-19 >>Matar gwamnan Kaduna

Nima yau zanje amin gwajin cutar Coronavirus/COVID-19 >>Matar gwamnan Kaduna

Kiwon Lafiya
Matar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail Elrufai ta godewa 'yan Najeriya bisa addu'o'in da suke ma mijinta da fatan Alheri.   Tace yana nan ba tare da wata alamar cutar ta nuna a tattare dashi ba. Saidai tace itama ta kebe kanta. https://twitter.com/hadizel/status/1244173126008737793?s=19 Tace a yaune itama zata je a gwadata.   A jiyane dai gwamnan ya bayyana cewa ya kamu da cutar ta Coronavirus/COVID-19.
Gwamnan Kaduna ya kamu da Cutar Coronavirus/COVID-19

Gwamnan Kaduna ya kamu da Cutar Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa Annobar cutarnan data addabi Duniya ta Coronavirus/COVID-19 ta kama gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.   Gwamnan da kansa ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta inda yace ya killace kansa.   Yace zai ci gaba da magana daga inda yake kuma mataimakiyar gwamnan zata ci gaba da kula da al'amuran yaki da cutar a jihar.   https://twitter.com/GovKaduna/status/1243979535021981696?s=19 Munai ma gwamna da sauran duk wanda suke fama da wannan cuta fatan Allah ya sauwake ya kuma dakile yaduwarta.
Yanzu-Yanzu:Gwamnatin jihar Kaduna ta kama limamai 2 da suka jagoranci sallar jam’i

Yanzu-Yanzu:Gwamnatin jihar Kaduna ta kama limamai 2 da suka jagoranci sallar jam’i

Uncategorized
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama wasu limamai 2 da suka jagoranci sallar jam'i duk da hanin da aka yi.   Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta shafinshi na sada zumunta ya bayyana cewa malaman masu sunan Malam Aminu Umar Usman da Malam Umar Shangel za'a gurfanar dasu gaban kiliya dan yanke musu hukunci.   https://twitter.com/GovKaduna/status/1243925277459320838?s=19   A lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar hana taro ta bayyana cewa duk wanda ya taka dokar za'a hukuntashi.   Gwamnan yace limaman sun take dokar jihar Kaduna ta rigakafin kare lafiyar al'umma
Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar zaman gida Dole

Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar zaman gida Dole

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar zaman gida na Dole inda tace gaba dayan jama'ar jihar zasu zama a killace.   Mataimakiyar gwamnan jihar,Hajiya Hadiza Balarabe ce ta sanar da haka inda tace shawarar kwararrune dake kula da yanda lamurran cutar ke gudana a suka bayar aka dauka.   Tace maganar rufe makarantu ta yi aiki amma jama'a na ci gaba da taro da kuma gudanar da ayyukan ibada wanda kuma a baya gwamnatin ta fada cewa idan ba'a bi shawarar data bayar ba to zata saka dokar ta baci.   Gwamnatin tace to an kawo lokacin da zata saka dokar.   Ta kara da cewa dokar zata fara aikine da karfe 12 na daren yau sannan kowane kasuwanci za'a rufeshi.   Motocin dake kai mai gidajen mai da jami'an tsaro dana lafiya basa cikin wannan doka da kum...
Hotuna: ‘Yan kasuwar Kaduna sun yiwa dokar gwamnati biyayya

Hotuna: ‘Yan kasuwar Kaduna sun yiwa dokar gwamnati biyayya

Siyasa
Kasuwannin ceceniya/Sheikh Abubakar Gumi duk a kulle, 'yan kasuwar Bacci ma basu fito ba.   Masu sufuri, motoci da babura da tafiya ciki da wajen Kaduna na ci gaba da aiki.   'Yan kasuwar sayar da kayan Mota sunce suna tunanin bandasu.   Bankuna na aiki.   Shafin hutudole ya zagaya cikin garin Kaduna dan duba yanda sabuwar doka me tsauri da gwamnatin jihar ta saka dan kare yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 ke aiki. A jiyane dai gwamnatin jihar Kadunan ta saka dokar kulle kasuwanni in banda masu sayar da abinci da magunguna sannan ta baiwa ma'aikata daga mataki na 12 umarnin zama a gida nan da kwanaki 30.   Gwamnatin ta kuma ce zata tursasa dokar hana taruwar jama'a da yawa wadda a farko ta bada shawara amma wasu suka ki bi. San...