
A lokacin baya da muka rika jawo hankalin gwamnati kan matsalar tsaro an ce mu makiyan Buhari ne>>Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu sani, tsohon sanata dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya bayyana cewa an rika musu fassarar cewa su makiyan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ko kuma suna so su bata sunansa a idon 'yan Najeriya yayin da suka rika bayyana magsalar tsaro.
Yace a lokacin suna majalisa, sun rika kokarin jawo hankalin shugaban kasar kan magsalar tsaro a Kaduna, Zamfara da Katsina tun bata kai haka ba.
Yace amma na kusa da shugaban kasar sun rika gaya masa cewa su makiyansa ne ko kuma suna son bata masa sunane.
Yace idan ba'a dauki mataki ba akwai matsala nan gaba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Sunnews inda yace kuma baya nadamar duk abinda yayi lokacin yana sanata.
A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda Gw...