fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Tag: kaduna

Bama Bakin ciki da mukaman da gwamnatin Kaduna ta ba Sarki Sanusi zata iya bashi duk mukamin da take so>>Gwamnati  Kano

Bama Bakin ciki da mukaman da gwamnatin Kaduna ta ba Sarki Sanusi zata iya bashi duk mukamin da take so>>Gwamnati Kano

Siyasa
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa bata bakin ciki da sabbin mukaman da gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa hambararren sarkin Kano,Muhammad Sanusi II.   Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya baiwa Sarki Muhammad Sanusi II mukami a kwamitin kula da zuba jari na jihar. Ya kuma karawa sarkin mukamin shugaban jami'ar jihar ta Kaduna,KASU.   Da Punch ke tambayar hadimin gwamnan kan kafafen watsa labarai da Sadarwa, Salihu Tanko Yakasai ko me zasu ce kan wannan lamari?   Sai ya kada baki yace basu da matsala da mukaman da gwamnatin jihar Kaduna ta ba sarkin kuma basa bakin ciki da hakan.   Ya kara da cewa gwamnatin Kaduna na da hurumin yin hakan.
Gwamnan Kaduna ya baiwa Habararren Sarkin Kano Sanusi mukami a gwamnatinsa

Gwamnan Kaduna ya baiwa Habararren Sarkin Kano Sanusi mukami a gwamnatinsa

Siyasa
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya nada tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi mataimakin shugaban hukumar KADIPA, dake da hakkin kula da hannaye jari da bunkasa tattalin arzikin jihar.   A sanarwan da Kakakin gwamna El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata, El-Rufai ya ce gwamnati ta zabo kwararru a harkar sanin tattalin arziki da saka jari kafin ta sanar da mambobin wannan hukuma.   Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe ce zata shugabanci wannan Hukuma, shi kuma tsohon sarki Sanusi a matsayin mataimakin wannan hukuma.   Ga sauran Mambobin 1. Her Excellency, Dr. Hadiza Balarabe Chairman 2. His Highness, Muhammadu Sanusi II Vice-Chairman 3. Balarabe Abbas Lawal, Secretary to the State Government 4. Bariatu Y. Mohammed, Head of Ser...
Kotu ta dakatar da gwamnan Kaduna daga rushe gidaje

Kotu ta dakatar da gwamnan Kaduna daga rushe gidaje

Siyasa
Wata babbar kotun jihar Kaduna wacce Mai shari'a Binta Zubairu ke jagoranta ta bayar da umarnin dakatar da gwamna Nasir El-Rufai da duk wani jami'in gwamnati daga rushe gidaje sama da 2,000 a garuruwan Nisi da Tasu na karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.   Daily trust ta rawaito cewa al’ummomin biyu suna da gidaje sama da 2,000 wadanda ke da adadin mutane sama da 10,000, majami’u 25 da makarantu 14.   Al'ummomin yankin Sun kai kara kotun ne ta hannun kungiyar lauyoyin da Sam Atung Esq ya jagoranta tare da neman kotu ta ba da umarnin dakatar da rushe musu gidaje.   Barrister Atung ya fadawa manema labarai jim kadan bayan an dage sauraren karar zuwa 30 ga Maris cewa wasu daga cikin gidajen suna da amincewar hukumomin gwamnati da suka dace a jihar, yana mai...
Gwamnatin Kaduna ta ba ‘yan kasuwar barci kwanaki 3 su tashi

Gwamnatin Kaduna ta ba ‘yan kasuwar barci kwanaki 3 su tashi

Uncategorized
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da wa'adin kwanaki uku ga masu shaguna a kasuwar barci a jihar da su tattara su bar kasuwar a wata sanarwa da ta fitar.   Mazauna kasuwar sun tarar da sanarwar ne a safiyar Asabar a shagunansu inda sanarwar ke cewa gwamnatin ta ba kowa kwanaki uku kowa ya bar kasuwar. Tun a kwanakin baya ake rade-radin cewa gwamnatin jihar za ta rushe kasuwar domin sauya mata fasali zuwa tsarin kasuwa ta zamani.   A takardar sanarwar, an bukaci masu rumfuna a kasuwar da su cire rumfunansu da kansu ko kuma su fuskanci fushin hukuma.   Yan kasuwar da dama sun koka dangane da wannan mataki inda wasu ke cewa an basu wa'adi a kurarren lokaci.   Malam Yahaya, wani mai shagon siyar da tufafi ne a kasuwar kuma ya shaida mana cewa akas...

An gano likitan da ya kwashe shekaru 11 yana aiki da takardun Bogi a Kaduna

Kiwon Lafiya
Ma’aikatar shari’a ta jihar Kaduna ta tuhumi wani likita da ake zargin yana amfani da takaddun bogi, mutumin mai suna.   Saidu Ahmed Ya’u, an gabatar dashi a gaban wata kotun majistare saboda amfani da satifiket din jabu da aikata ba daidai ba. A wata sanarwa da ma’aikatar shari’ar, wacce babban lauyan gwamnatin jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta sanya wa hannu, ta ce, ana ci gaba da tsare wanda ake zargi a Cibiyar Kula da gyaran hali dake Kaduna har zuwa 16 ga Maris. Sanarwar ta kara da cewa Rahoton Bayanai na Farko (FIR) ya nuna cewa Saidu ya kasance yana aiki a matsayin likita sama da shekaru 11 a matsayin ma’aikacin sashin lafiya. A cewar babbar lauyan gwamnatin, gwamna Nasir El Rufai ya umarci ma’aikatar kiwon lafiya da ta binciki Saidu, biyo bayan wata takadda...
Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mutane Sama Da Hamsin A Kaduna

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mutane Sama Da Hamsin A Kaduna

Uncategorized
A jiya Lahadi, wasu 'yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Igabi ta Jahar Kaduna. Kauyukan da abin ya shafa sun hada da , Zareyawa, Marina dake gundumar Kerawa inda suka hallaka mutane 51 suka jikkata wasu sannan suka kone motoci da dama. Majiyarmu ta shaida mana cewar maharan sun kai samamen ne da Asuba musalin karfe 6:00 ana idar da sallar Asuba. RARIYA ta sami rahoton cewar mafi yawan 'yan kauyukan sun gudu yayin da maharan suka kona gidaje da dama sannan suka yi awon gaba da kayan masarufi (abinci). Kansilan gundugumar Kerawa, Malam Dayyabu Kerawa ya tabbatarda aukuwar lamarin ga wakilin Daily Trust kuma ya kara da cewa an burne mutum 51 da suka rasa rayukansu da misalin karfe 4 : 00 ma yamma.

Gwamnan jihar Kaduna ya zama abin koyi ga sauran gwamnonin kasarnan akan gyaran Ilimi

Uncategorized
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya zama abin koyi ga sauran gwamnonin jihohin kasarnan musamman Arewa, akan yiwan malaman firaimare jarabawa da kuma tantance wadanda suka cancanta sannan a sallami wadanda basu cancantaba. Kwanannan ne gwamnan ya shiryawa malaman firaimare na jihar jarabawar ' yan aji hudu amma sakamakon jarabawar ya nuna cewa guda dubu ashirin da biyu sun fadi kuma gwamnan zai sallamesu aiki ya dauki wasu sabbin malam su dubu ashirin da biyar. Wannan batu ya dauki hankulan mutane sosai inda wasu dake tausayawa malaman da za'a kora suka bayyana cewa bai kamata a koresuba, kamata yayi a basu horaswa ta musamman ko kuma a mayar dasu wata ma'aikatar inda ba zasuyi koyarwa ba, tunda ba dadi mutum da iyali a kulle mishi hanyar samu. Wasu kuma sun bayyana cewa t...

Kalaman Sanata Shehu Sani akan korar malaman jihar Kaduna daga aiki sun jawo cece-kuce

Uncategorized
 Sanata Shehu Sani me wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayya yayi wasu rubuce-rubuce da suka dauki hankulan mutane suka kuma jawo cece-kuce a dandalinshi na sada zumunta da muhawara da shafin Twitter. Sanatan yayi maganane akan batun da wata kididdiga da akayi ta nuna cewa 'yan sandan Najeriyane na daya a Duniya wajan rashin yin aiki yanda ya kamata, sanatan yace wasu zasu iya cewa a kori 'yan sandanmu daga aiki tunda ance basu iya aikiba, ban yarda da irin wannan ra'ayiba. Duka da dai sanatan be kama suna ba amma mutane da yawa sun fahimci cewa da gwamnan jihar Kaduna yake akan batun sallamar malamai da yace zaiyi bayan da aka musu jarabawar 'yan aji hudu mafi yawanci su suka kasa cin jarabawar. Masu sharhi da damane suka bayyana cewa be kamata sanata Shehhu Sani ya ...