
An biya Kudin fansa kamin aka sake mu>>Daliban Kankara suka bayyana
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa bata biya masu garkuwa da mutane da suka sace daliban Kankara ko sisi ba kamin suka sakesu.
Saidsi wasu daga cikin daliban sama da 300 sun bayyanawa, WSJ cewa 'yan Bindigar dake tsare dasu sun gaya musu cewa sai da aka biya kudin fansa kamin aka sakesu.
Wani daga cikin daliban, Yinusa Idris ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bayyana musu cewa an biyasu Miliyan 30 dan su sakesu amma suka ce ba zasu sakesu ba saboda Miliyan 344 suka nema, watau kowane dalibi za'a biya masa Miliyan 1.
Yace dan haka sai suka ware dalibai 30 suka ce su kadai zasu saki, inda suka daukesu a mashina.
Wani Imrana Yakubu shima ya bayyana cewa Masu garkuwa da mutane sun gaya musu idan ba'a biya kudin fansar da suka nema ba ...