Monday, March 30
Shadow

Tag: kannywood

Allah ya baka lafiya>>Ali Nuhu yawa Gwamna El-Rufai addu’a

Allah ya baka lafiya>>Ali Nuhu yawa Gwamna El-Rufai addu’a

Kiwon Lafiya
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu sarki ya jajantawa Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bisa cutar Coronavirus data kamashi.   A wani sako daya wallafa a shafinsa na sada zumunta,Ali Nuhu yace   Allah ya baka Lafiya mai girma Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Ya kuma kare dukkan al'umma da wannan cutar ta Covid-19. Jama'a a daure a Zauna a gida kuma a rage cudanya cikin taron mutane. Allah ya karemu baki daya. https://www.instagram.com/p/B-WgHQHh2-V/?igshid=1awepqcqb9j99   Gwamna El-Rufai na daga cikin manyan mutanen Arewa da cutar ta kama kuma tuni ya bayyana cewa ya killace kansa.
Wasu sanannun mutane sai su saka cewa a zauna a gida a shafukansu na sada zumunta amma sai ka gansu a waje>>Nazir Sarkin Waka

Wasu sanannun mutane sai su saka cewa a zauna a gida a shafukansu na sada zumunta amma sai ka gansu a waje>>Nazir Sarkin Waka

Nishaɗi
Tauraron mawakin Hausa,Nazir Ahmad Sarkin Waka kenan a wannan bidiyon nasa inda yake magana kan sanannun mutanen dake sakawa a shafukansu cewa a zauna a Gida.   Yace irin wadannan sanannun mutane bayan sun saka wancan abu a shafinsu na sada zumunta kuma kawai kana kan layi sai ka hadu dasu.   https://www.instagram.com/p/B-NQvjjpB9q/?igshid=1i5lnshqu55xa     Nazir daiyayi wannan magana yana nishadi ba tare da ya bayyana da wa yake ba.
FARGABAR CORONAVIRUS: Zaharadden Sani ya killace kansa na kwana biyu

FARGABAR CORONAVIRUS: Zaharadden Sani ya killace kansa na kwana biyu

Nishaɗi
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Kannywood ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES a Kaduna cewa fargaban gwajin jinin Ali Nuhu da aka ce za ayi kan cutar coronavirus ya dimauta shi har ya killace kansa nan da nan.     Zaharaddeen ya ce har ya dan yi wasiyyoyi ga iyalan sa cewa to ta-fa faru ta Kare, domin kila ya kamu da cutar coronavirus.     Babban dalilin fadin haka kuwa shine ya na daga cikin wadanda suka yi cudanya da Ali Nuhu a wadannan kwanaki.     ” Ali Nuhu jarumi ne a sabon fim dina da na gama dauka mai suna Haduwar Hanya.     ” Mun tafka mu’amula da cudanya matuka tare, kaga ko idan kaji irin haka dole hankalin ka ya tashi.     Zaharaddeen ya ce yana jin haka sai ya koma gida ya killace
Hotuna: Rahama Sadau ta kulle kasuwancinta Saboda Coronavirus/COVID-19

Hotuna: Rahama Sadau ta kulle kasuwancinta Saboda Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan inda take tare da ma'aikatanta dake aiki a gidan abincinta.   Rahama ta bayyana cewa ta kulle shagon sayar da abincin nata saboda annobar COVID-19 kuma ta damu da lafiyar ma'aikatanta da abokan hulda.   https://www.facebook.com/931269690271728/posts/2843197485745596/   An ga Rahama Sadau da ma'aikatan nata sanye da Abin kariyar Hanci.
Cutar COVID-19: MOPPAN ta dakatar da shirya finafinai

Cutar COVID-19: MOPPAN ta dakatar da shirya finafinai

Kiwon Lafiya
SAKAMAKON ɓarkewar muguwar cutar nan ta 'Coronavirus', uwar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa, wato 'Motion Picture Practitioners Association of Nigeria' (MOPPAN), ta hana aikin shirya kowane irin fim a arewacin Nijeriya baki ɗaya.   Cutar, wadda a taƙaice ake kira 'COVID-19', ta na ta kashe bil'adama a yawancin ƙasashen duniya a yanzu, ciki har da Nijeriya.   Mujallar Fim ta ruwaito cewa gwamnatocin ƙasashe da na jihohi da sauran wuraren ayyuka da cuɗanya da juna sun bada umarnin cewa mutane su killace kan su kuma su ɗau matakan kariya don hana yaɗuwar cutar.   A cikin wata sanarwa da shugaban MOPPAN na ƙasa Dakta Ahmad Muhammad Sarari ya fitar a yau, kuma aka ba mujallar Fim, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin hana cigaba da yaɗuwar cutar.
A yiwa dokar zama a gida biyayya a kuma rika wanke hannu>>Amina Amal ga Masoyanta

A yiwa dokar zama a gida biyayya a kuma rika wanke hannu>>Amina Amal ga Masoyanta

Kiwon Lafiya
Tauraruwar fina-finan Hausa, Amina Amal ta jawo hankalin masoyanta kan yiwa dokar da hukumomi suka saka biyayya dan maganin yaduwar cutar Coronavirus.   Da take magana a wani gajeren bidiyo data saka a shafinta na Instagram, Amina tace a yi hakuri a zauna a gida a kuma a rika wanke hannu.   https://www.instagram.com/p/B-MESL6F86y/?igshid=s6hm2tic4s53   Amina ta kara da cewa a saka abin rufe fuska da kuma saka safar hannu yayin amfani da na'urar cire kudi ta ATM.
Coronavirus: Duk shugaban da ya hana jam’in Sallah ya tanadi abinda zai gayawa Allah>>Ado Gwanja

Coronavirus: Duk shugaban da ya hana jam’in Sallah ya tanadi abinda zai gayawa Allah>>Ado Gwanja

Kiwon Lafiya
Tauraron fina-finan Hausa kuma mawakin Mata, Ado Isa Gwanja ya dauki hankula sosai, Musamman a shafukan sada zumunta bayan maganar da yayi akan cutar Coronavirus.   Gwanja yayi maganane akan hana sallah a jam'i da hukumomin wasu jihohi suka saka dan dakile yaduwar cutar ta Coronavirus.   A wani faifan bidiyo da tuni ya watsu sosai, Gwanja yace duk shugaban da ya hana sallah saboda Coronavirus to ya tanadi abinda zai je ya gayawa Allah. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1242762693142077442?s=19 Ya kuma kara da cewa shi idan duk cutar Duniyarnan zata taru akan mutum ba zai hanashi zuwa tayi sallah ba dan yasan inda zashi daga nan.    
Coronavirus: Duk wanda Allah ya kaddaro zata kama sai ta kamashi, Addu’a ya kamata mu yi>>Lawal Ahmad

Coronavirus: Duk wanda Allah ya kaddaro zata kama sai ta kamashi, Addu’a ya kamata mu yi>>Lawal Ahmad

Kiwon Lafiya
Tauraron fina-finan Hausa,Lawal Ahmad ya jawo hankulan mutane kan Annobar cutar Coronavirus inda yace abu mafi a'ala shine a rike Addu'a.   Lawal ya bayyana hakane a shafinshi na Instagram inda yace mutum kawai yayi Imani da kaddara. Domin duk wanda allah ya kaddara zai samu cutar ba zai guje mata ba.   https://www.instagram.com/p/B-H8VLclsDq/?igshid=awasijv1b1xa   A yanzu dai yawan masu dauke da cutar Coronavirus a Najeriya ya kai 51 inda mutum 2 suka warke, 1 kuma ya mutu.