Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya nuna Hoton wata Masoyiyar sa da yace sunanta Hafsa.
Yace ta hadu dashi kuma saboda murna, sai da ta yi sujadar Godiya ga Allah. Nura ya kara da cewa yana mata fatan Samun Miji na gari.
Ana ci gaba da daukar shirin fim din Labarina me farin jini wanda aka nunashi a gidan Talabijin na Arewa24.
Daya daga cikin taurarin fim din, kuma shahararren mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Waka, ya bayyana cewa an sakashi ya aske sumarsa.
Ya bayyana cewa ya Aske sumarsa ne saboda masu shirya Fim din na Labarina sun bukaci haka, amma fa sai da suka biyashi, kuma ba aske ta gaba daya yayi ba, an dai rageta ne.
Yace shekara guda kenan be taba ta ba taba.
Dan kallon Bidiyon a danna nan
Tauraron Fina-finan Hausa, Mustapha Nabraska ya samu karuwa inda aka haifa masa diya mace.
Ya sanar da hakanne a shafinsa na sada zumunta inda yace hakan ya farune a jiya, Juma'a.
Muna tayashi murna da fatan Allah yawa rayuwarta Albarka.
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu na murnar zagayowar ranar Haihuwarsa.
Ali ya cika shekara 47 a yau. Kuma abokan aiki da 'yan uwa da abokan arziki sai tayashi murna suke.
Sani Musa Danja, Nafisa Abdullahi, da sauransu na daga cikin wanda suka taya Ali murna. Muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.
Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa,Mansurah Isah ta bayyana takaicinta kan yanda aka rasa samun nuna halin damuwa da sace dalibai da akw a Arewa.
Ta tambayi cewa shin 'yan Legas ne kadai zasu iya yakar gwamnatin Najeriya da kawo Canji, saboda Su kadai gwamnati take jin tsoro.
Tace suna fitowa su bayyana samuwarsu ba tare da fargaba ba, kuma kana taba daya daga cikinsu kamar ka taba dukansu ne, basa yacewa juna baya.
Tace babu Munafurci ba Kyashi ba bakin ciki. Tace ana magana yanzu, ko wani abune ya sameka, musulmi dan uwanka ne zai fara cewa Allah kara, kadan ma ya gani, Allah kara mishi Musiba. Tace da sune aka sace yara a Makaranta, ai da yanzu sun hana gwamnati bacci, da sun ta yayata abin a shafukan sada zumunta ta yanda kasar Amurka tuni zata ...
Tauraruwar fina-finan Hausa,Hadiza Gabon ta saka kayataccen hoton Bidiyon ta tare da diyarta da take riko, watau Maryam suna nishadi.
Ta saka hoton ne a shafinta na sada zumunta wanda ya dauki hankula sosai akai ta yabawa.
Saidai daga baya Hadizar ta gogeshi.
Tauraruwar fina-finan Hausa,Fati Washa kenan a wadannan hotunan nata data Haskaka.
Ta sakawa Masoyanta Hotunan a shafinta na sada zumunga inda kuma da dama suka yaba.
A jiya ne dai hutudole ya kawo muku rahoton yanda surukin shugaban kasa, Ahmad Indimi dake auren diyar shugaban kasar, Zahra Buhari tare da zakinsa da ya siya wanda zai rima kiwo.
Wannan lamari ya dauki hankula sosai musamman a shafukan sada zumunta inda ake ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa'a itaka ta bayyana ra'ayinta kan wannan batu, inda tace babu Amana tsakanin Mutum da Kura, tace Ahmad ya daina dan kuwa suna sonshi ko dan Zahara.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wadannan kayatattun hotunan nata data dauka a cikin jirgin sama na musamman.
Ta sakawa masoyanta Hotunan a shafinta na sada zumunta inda da dama suka yaba.