fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Kano al’majirai

Al’majirai 28 ne suka harbu da cutar coronavirus – A cewar Gwamnatin Jihar Kano

Al’majirai 28 ne suka harbu da cutar coronavirus – A cewar Gwamnatin Jihar Kano

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kano ta ce Almajrai 1,146  da aka dawo dasu jihar, bayan yi musu gwajin cutar Covid-19 an samu al'majirai 28 masu dauke da cutar, a rahoton da jaridar PUNCH ta rawaito. Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa, da kwamishinan kananan hukumomi na jihar, Murtala sulen Garo ya sanar a ranar laraba. Inda yace “Mun dauki Almajirai 419 zuwa jihar Katsina, 524 zuwa jihar Jigawa, 155 zuwa jihar Kaduna, 38 zuwa jihar Bauchi, sannan 36 ga jihar Gombe. Yayin da muka karbi al'majirai 179 daga jihar Adamawa, 220 daga jihar Nassarawa, 96 daga jihar Gombe, 18 daga jihar Katsina, 92 daga jihar Kaduna. Daga cikin al'majirai 1,266 da aka gwada su an samu 28 masu dauke da cutar COVID-19,  Yayinda aka gano 311 dauke da wasu cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, ciwon ciki. haka zalika...
Gwamnatin jihar kano ta shirya sallamar al’majirai 2000 da aka kebe a ranar litinin

Gwamnatin jihar kano ta shirya sallamar al’majirai 2000 da aka kebe a ranar litinin

Kiwon Lafiya
A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnatin Jihar Kano ta ba da tabbacin cewa sama da Almajiris 2000 dake killace a cibiyoyin killa cewa dake kiru da karaye za a sallame su a ranar litinin 18 ga watan mayu. Kwamishinan Ilimi na Jiha kuma Shugaban Kwamitin Kula da ‘Yan makaranta Almajiris Muhammadu Sanusi Kiru ne ya tabbatar da hakan ga Solacebase a ranar Lahadin da ta gabata yayin ziyarar cibiyoyin biyu a kananan hukumomin Kiru da Karaye inda sama da Almajiri 2000 suka keɓe. Muhammadu Sanusi Kiru ya ce an dawo da mafi yawan Almajirin ne daga wasu jihohin kuma za a mika su ga iyayensu a kananan hukumomi daban-daban na jihar. A cewar sa duk da haka wasu daga cikinsu wadanda ke nuna alamun rashin lafiya za a ware su kafin a mayar da su ga iyayensu," in ji Alhaji Kiru. Kwamishinan ya...