
Mutum na farko da ya harbu da cutar Coronavirus a jihar Kano Ambasada Kabiru Rabi’u ya warke daga cutar
Kabiru Rabi’u, ya warke sarai daga cutar bayan doguwar jinya da ya sha kuma har an sallame shi daga cibiyar killace masu dauke da cutar da jihar Kano ta tanada a Kwanar Dawaki.
Dan Ambasada Kabiru Rabi’un, mai suna Abba, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Lahadi.
Abban ya ce an sallami mahaifin nasa ne da safiyar yau tun bayan da aka killace shi a ranar 11 ga watan Afrilu, 2020.
Kafin killace Ambasada Kabiru Rabi’u, ya yi tafiye-tafiye zuwa Legas, Abuja da Kaduna, inda ya dawo Kano a ranar 25 ga watan Maris, 2020 yana fama da ‘yar rashin lafiya.
Zuwa yanzu dai jihar Kano na da adadin mutane 576 da aka tabbatar sun harbu da Coronavirus. Daga cikin wannan adadi, mutane 32 sun warke har an sall.