fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Kano covid19

Covid-19: Jihar Kano ita ce jiha da tafi yawan masu warkewa daga cutar Korona >> NCDC

Covid-19: Jihar Kano ita ce jiha da tafi yawan masu warkewa daga cutar Korona >> NCDC

Kiwon Lafiya
An bayyana Jihar Kano a matsayin jihar da ta yi fintinkau wajen yawan adadin masu samun waraka daga cutar Coronavirus, hakan na bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cutuutuka a Najeriya wato NCDC. A rahoton da hukumar lafiya ta jihar ta fitar ta bayyana cewa jihar ta samu karin mutum 3 wadanda suka kamu da cutar Korona a cikin adadin mutum 152 da aka gwada, Wanda ya kawo adadin mutum 1,271 masu dauke da cutar a fadin jihar. Haka kuma jihar ta sallami adadin mutum 1,029, tare sa samun mutuwar mutum 52. Kamar yadda jaddawalin rahoton da hukumar ta wallafa. https://twitter.com/KNSMOH/status/1280630714225119234?s=20   Haka zalika a wani labarin duka daga jihar Kano Maigirma Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike da neman amincewar Majalisar Dokokin jihar domin ...
Bayan cire dokar zaman gida Jihar Kano ta kara sallamar mutum 26 wanda suka warke daga cutar Korona

Bayan cire dokar zaman gida Jihar Kano ta kara sallamar mutum 26 wanda suka warke daga cutar Korona

Kiwon Lafiya
A ranar Al'hamis ne gwamanatin jihar kano ta ayyana janye dokar zaman gida a fadin jihar gaba daya. Wanda ya baiwa al'ummar jihar damar yin zirga zirga a ko wanne lokaci da suke bukatar hakan. Sai dai  a rahoton da Ma'aikatar lafiya ta jihar ta wallafa ta bayyana kara samun mutum 5 wanda suka harbu da cutar corona bayan an sallami karin mutum 26 wadanda suka warke garau daga cutar.   https://twitter.com/KNSMOH/status/1279186988726456325?s=20   Ya zuwa yanzu jihar kano tana da adadin mutum 1,262 masu dauke da cutar a jihar inda kuma aka sallami mutum 1,003.
Gwamna Ganduje ya bayyana matsayar gwamnati akan bude makarantun jihar

Gwamna Ganduje ya bayyana matsayar gwamnati akan bude makarantun jihar

Kiwon Lafiya
Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya bayyana matsayar gwamnatin jihar kano kan makarantun jihar da ke cigaba da ka sancewa a rufe tun tsawan lokacin da aka sanya dokar zaman gida a jihar a sakamakon bullar cutar Korona. Gwamna ganduje ya bayyana cewa dukkan makarantun jihar zasu cigaba da kasancewa a rufe har zuwa wani lokaci da gwamnati zata bayyana, A ranar Al'hamis ne gwamnatin jihar ta janye dokar zaman gida data sanya wanda ya shafe tsawan lokaci. Bayan soke dokar zaman gida da gwamnatin jihar tai, haka zalika gwamnatin jihar ta Umarci ma'aikatan gwamnati da su koma bakin aiki su a ranar litinin.
Jihar Kano ta sallami karin mutane 31 bayan sun warke garau daga cutar coronavirus/covid-19

Jihar Kano ta sallami karin mutane 31 bayan sun warke garau daga cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar lafiya ta jihar kano ta sanar da sallamar karin mutum 31 bayan sun warke daga cutar corona, haka zalika jihar ta kuma tabbatar da samun karin mutun 5 wanda suka harbu da cutar. Ma'aikatar ta bayyana adadin samfuran da cibiyar yaki da cututtuka dake jihar ta gwada inda cibiyar ta gwada adadin samfuran mutum 327 daga bisani aka samu mutum 5 wanda suka kamu da cutar.   https://twitter.com/KNSMOH/status/1277361886787403776?s=20 Baya ga haka jihar ya zuwa yanzu nada adadin mutum 1,200 da suke dauke da cutar a jihar, sannan an samu mutuwar mutum 51.
Kwalejin kimiyya da kere kere ta jihar Kano ta samar da abun tsaftar hannu mai aiki da kansa

Kwalejin kimiyya da kere kere ta jihar Kano ta samar da abun tsaftar hannu mai aiki da kansa

Kiwon Lafiya
Kawlejin kimiyya da kere kere dake jihar Kano, wanda aka sani da Kano state polytechnic ta samar da abun wanke hannu mai aiki da kansa. An samar da abun tsafatar hannun ne domin dakile yaduwar cutar coronavirus. Gwamnan jihar Kano tare da makarrabansa sun ganewa idanun su yadda abun ke aiki.   An dai tsara abunne wanda dazarar ka sanya hannun ka a kasan kan famfan nan take zai zubama man wanke hannnu, daga bisani sai ya zuboma ruwa mai tsafta don wanke hannayan naka.  
Covid-19: Gwamnatin jihar Kano ta yi barazanar hukunta Makarantun Islamiyyu  wadanda suka karya doka wajan bude Makarantu a jihar

Covid-19: Gwamnatin jihar Kano ta yi barazanar hukunta Makarantun Islamiyyu wadanda suka karya doka wajan bude Makarantu a jihar

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kano ta yi barazanar hukunta wasu makarantun islamiyyu wadanda suka  karya doka wajan bude Makarantu a jihar. Hakan na kunshe ne ta cikin jawabin da kwamishinan ilimi na jihar ya bayyana ga manema labarai a wata zantawa da yayi a wani gidan radiyo dake jihar kano. Kwamishinan ilimi na jahar Kano Sunusi Maji Dadin Kiru ya bayyana cewa zasu hukunta duk wani malami da aka kama ya karya doka wajen bude makarantun islamiyya A jahar Kano. Ya kuma kara da cewa bude makarantun islamiyoyi a wanan lokacin zai jefa rayuwar dalibai cikin hatsari inda ya gargadi malaman makarantun islamiyoyi da kada wanda ya kuskura ya bude makaranta har sai hukumar ilimi ta jahar Kano ta bada umarnin hakan. Kwamishinan ya kuma Kara nanata cewa "Duk wanda muka Kama ya karya Mana doka zamu da...
Jihar Kano ta sallami karin mutum 25 wadanda suka warke daga cutar coronavirus/covid-19

Jihar Kano ta sallami karin mutum 25 wadanda suka warke daga cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da samun karin mutum 5 wanda suka harbu da cutar coronavirus bayan gwajin mutum 179. Ma'aikatar ta Kara da cewa ta sallami karin mutum 25 wadanda suka warke garau daga cutar a jihar. Sanarwar hakan ta fitone ta cikin shafin hukumar data wallafa.   https://twitter.com/KNSMOH/status/1270850167432982530?s=20 Ya zuwa yanzu jihar kano ta sallami adadin mutum 522.
Wani mai cutar coronavirus/covid-19 ya rasu a jihar kano

Wani mai cutar coronavirus/covid-19 ya rasu a jihar kano

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar lafiya ta jihar kano ta sake fidda sanarwar Kara samun sabbin wanda suka harbu da cutar coronavurus a jihar, inda jihar ta samu akalla karin mutum 5. Ma'aikatar ta kuma sanar da kara sallamar adadin mutum 27 wadanda aka tabbatar da sunwarke garau daga cutar, wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama ya kai kimanin mutum 477. https://twitter.com/KNSMOH/status/1270126978549645312?s=20 Haka zalika jihar ta kara samun karin mutuwar mutum 1 wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu a sakamakon cutar a jihar ya kai 49.  
Jihar kano ta kara sallamar mutum 32 wanda suka warke daga cutar coronavirus/covid-19

Jihar kano ta kara sallamar mutum 32 wanda suka warke daga cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar lafiya ta jihar kano ta fitar da sanarwar cewa bayan gudanar da gwajin mutum 5,002 da tayi kuma tai nasarar sallamar karin mutum 32 wanda suka warke garau daga cutar coronavirus. Kamar yadda hukumar lafiya ta bada sanarwar hakan a jiya. https://twitter.com/KNSMOH/status/1268316223424679937?s=20 A yanzu dai jihar kano nada adadin mutum 970 baya ga sallamar mutum 318 sannan an samu mutuwar mutum 45.
Jihar kano tai nasarar sallamar mutum 40 wanda suka warke daga cutar coronavirus/covid19, mutum 2 sun mutu

Jihar kano tai nasarar sallamar mutum 40 wanda suka warke daga cutar coronavirus/covid19, mutum 2 sun mutu

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar lafiya ta jahar kano ta bada sanarwar sallamar adadin mutum 40 wanda suka warke daga cutar coronavirus a jihar.   Baya ga haka ma'aikatar ta fidda bayanin sake samun mutum 3 wanda suka harbu da cutar a jahar, tare da rahotan mutuwar mutum 2. https://twitter.com/KNSMOH/status/1267223235810164736?s=20 Yazuwa yanzu jahar nada adadin mutum 954 baya ga mutum 240 da aka sallama, sai kuma mutum 45 suka rigamu gidan gaskiya.