
Kotu ta daure wani mai safarar giya watanni 8 a gidan gyaran hali a jihar Kano
Wata kotun majastare dake da zamanta a jihar Kano ta daure Kube Bulus watanni 8 a gidan gyaran hali, ko kuma biyan tarar naira 70,000 a sakamakon kamashi da a kai da zafarar barasa.
Kotun dake zaune a Gasau a karamar hukumar Kumbotso ta samu Kube Bulus da laifin safarar giya daga sabon gari zuwa Panshekara dake birnin jihar kano.
Kwamandan hukumar hisba a karamar hukumar kumbotso Gwani Murtala ya shaidawa Hutudole cewa, hukumar ta cafke wanda a ke zargin ne a ranar Juma'a inda kuma ta gabatar da shi a gaban kotu a ranar litinin.
Kamar yadda ya shaida mana cewa "Hukumar ta cafke Bulus dauke da barasa a cikin babur mai kafa uku a yankin panshekara.
Haka zalika kwamandn ya bayyana cewa "giyar wacce ta kai ta kimanin Naira 400,000 an boye ta ne a cikin babur din a dai-dai...