fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Kano state

Hotuna: Tsohon Dan takarar Gwamanan Jihar Kano Lawan Jafaru Isa ya kai ziyarar girmamawa Fadar Sarkin Kano

Hotuna: Tsohon Dan takarar Gwamanan Jihar Kano Lawan Jafaru Isa ya kai ziyarar girmamawa Fadar Sarkin Kano

Uncategorized
Daga Jihar Kano Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Alhamis ya yakarbi Bakuncin Janar Lawal Jafa'ru Isa a fadarsa dake Masarautar Kano. Lawan Jafaru wanda ya taba rike.mukamin   gwamna a jihar Kaduna ya kuma tsaya takarar Gwamna a jihar Kano A tutar Jam'iyyar CPC Kafun rushewar Jam'iyyar.   Hakanan Mai martaba sarkin Kano Aminu Ado bayero a ranar Laraba Ya Halarci Bikin Saukar Al'Qur'ani Mai Girma Na Makarantar Tagrisu Hubbin Nabiyyi(S.A.W) Lil Hayatul Islamiyya Dake Tukuntawa a Karamar Hukumar Birnin Kan.
An kama wani matashi mai shekaru 20 da yayi niyyar sace yaro mai shekaru 2 a jihar Kano

An kama wani matashi mai shekaru 20 da yayi niyyar sace yaro mai shekaru 2 a jihar Kano

Tsaro
Lamarin dai ya faru ne a sabon gari dake jihar kano inda aka zargi wani matashi mai shekaru 20 da yayi kokarin sace wani yaro mai shekaru 2 da haihuwa. Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da kafar mu cewa, jami'an tsaro sunyi nasarar kubutar da matashin daga hannu wasu mafusata wadanda suka fara kokarin lakadawa matashin dokan kawo wuka. Matashin da ba'a bayyana sunan shi ba, sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa an hangi matashin a lokacin da ya ke kokarin guduwa da yaron wanda nan danan jama'a suka taru bayan an fallasa yun kurinsa. Daga bisani dai Jami'an tsaro sun yi nasarar tafiya da matashi zuwa ofishin su dake Nomansland domin amsa tambayoyi.