fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Kano yan kasuwa

Kano: Ganduje ya gayyaci shugabannin kasuwanni kan hauhawar farashin kayayyaki

Kano: Ganduje ya gayyaci shugabannin kasuwanni kan hauhawar farashin kayayyaki

Kasuwanci
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gana da shugabannin kasuwar a jihar kan hauhawar farashin kayayyakin masarufi. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan, Malam Abba Anwar, ranar Alhamis a Kano.   Anwar ya ce Ganduje, wanda ya gana da shugabannin kasuwar a gidan gwamnati, ya sanar da su wahalar da ‘yan kasa ke ciki sakamakon hauhawar farashin kayayyaki masu mahimmanci, la’akari da cewa watan Ramadana ne da kuma Coronavirus (COVID-19). Biyo bayan korafin da ‘yan kasuwar suka yi kan matsalolin samun kayayyaki da aiyukan, gwamnan ya yi masu alƙawarin cewa gwamnatin sa za ta yi duk iya ƙoƙarinta domin taimaka musu da rage ƙalubalen da suke fuskanta a harkokin kasuwancin su.   "Na ji duk korafinku, m...