fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Tag: kano

WAEC: Muhimmiyar Sanarwa ga Daluban dake Makarantun kwana A jihar Kano

WAEC: Muhimmiyar Sanarwa ga Daluban dake Makarantun kwana A jihar Kano

Uncategorized
Gwamnatin jihar kano ta sanar da hade makarantun kwana guda 33, A jihar zuwa cibiyoyi 12, ga Daluban dake shirin zana jarabawar karshe ta sakandire wato WAEC. Sakataran zartarwa na hukumar Ilimi na jihar (KSSSMB) Bello Shehu shine ya bada wannan umarnin a ranar Alhamis a taron da hukumar ta gudanar. Shehu ya bayyana cewa, An dauki matakin ne domin baiwa Daluban Ishash-shiyar kulawa a yayin jarabawar.   Ya kara da cewa Sauran makarantun Sakandire guda 161 na jeka ka dawo, za su zana jarabawar su, A makarantun su kamar yadda a ka saba, inda ya bayyana cewa, hade makarantun bai shafe su ba.     Jaddawalin Makarantun da a ka ware domin Daluban dake makarantun kwana a jihar, sune kamar haka:   GGUC Kachako, GGSS Sumaila, da GGSS Albasu zasu hallara a makarantar Gwamnati ta Gove
Ana bincikar hadimin gwamna Ganduje kan harkokin Adiinin Musulunci, Ali Baba kan karkatar da kudin malamai

Ana bincikar hadimin gwamna Ganduje kan harkokin Adiinin Musulunci, Ali Baba kan karkatar da kudin malamai

Siyasa
Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano na binciken me baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin addinin Musulunci, Ali Baba Fagge kan aikata ba daidai ba da wasu kudin malamai.   Jihar Kano ta tattaro malamai kusan 336 dan su yiwa Najeriya da jihar addu'o'in tsaro daga cutar Coronavirus wanda kuma aka baiwa Ali Baba kudin sallamar malaman. Saidai shugaban hukumar yaki da rashawar, Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana cewa sun samu korafi akan cewa an ragewa malaman kudin da ya kamata a basu.   Dan hakane yace aka kaddamar da bincike akansa da 'ya'yanshi wanda ake zargin sun taimaka mai wajan wannan aiki. Ana zargin dai ya cire Dubu 50 akan kudin da aka baiwa kowane malami, kamar yanda Daily Post ta ruwaito.
Ruwa ya ci wani matashi dake wanka a Kudiddifi a Kano

Ruwa ya ci wani matashi dake wanka a Kudiddifi a Kano

Uncategorized
Wani katashi me kimanin shekaru 27 ya nutse a ruwa ya mutu yayin da yake wanka a Kudiddifi a kauyen Rangaza Inusawa, dake Karamar Hukumar Ungwaggo a Kano.   Matashin, Abubakar Salisu, ya rasune da safiyar yau, Juma'a kamar yanda me magana da yawun hukumar kwana-kwana ta Kano, Malam Saidu Muhammad ya bayyana. Ya bayyanawa kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN cewa, da suka je, tuni gawar matashin har ta yi sama saidai ita suka kai Asibiti.
Hukumar Cin Hanci Da Rashawa ta Jihar Kano zata Binciki korafin da A ka shigar gabanta A kan Ali Baba

Hukumar Cin Hanci Da Rashawa ta Jihar Kano zata Binciki korafin da A ka shigar gabanta A kan Ali Baba

Tsaro
Hukumar Cin hanci da rashawa da karbar korafe korafe ta jihar Kano ta tabbatar da karbar korafin da wasu Malamai suka shigar hukumar bisa korafin da su kai kan Mai bawa gwamna shawara kan Addinai Ali Baba da cewa ya yanke musu wani kaso daga cikin kudadan da gwamna ya basu. Tun dai da Fari Gwamnatin jihar Kano ta gayyaci Malaman jihar domin su gudanar da addu'o'i a ranar Arafa domin neman kariya daga cutar Korona data addabi Kasar. Bayan kammala addu'o'in ne sai Mai baiwa Gwmanan Shawara Ali Baba ya tura dansa ya tsaya a kofar gidan gwamnati, inda ya ke karbar wani kaso daga cikin kudadan da gwamna ya baiwa Malaman, Kudadan da a ka baiwa Malaman sun kai kimanin Dubu Hamsim 50,000, inda rahotanni suka bayyana cewa, an karbe musu 5,000 daga cikin kudadan nasu. Sai dai bayan shiga...
Kungiyar CAN ta kai Wata Ziyara Ga Sarkin Karaye A jihar Kano

Kungiyar CAN ta kai Wata Ziyara Ga Sarkin Karaye A jihar Kano

Siyasa
Kungiyar CAN ta ziyarci Sarkin Karaye tare da yi masa gaisuwar Sallah Kungiyar kiristocin Najeriya CAN reshan karamar hukumar Kiru a jihar Kano sun kai wata ziyarar girmamawa Masarautar Kiru tare da yiwa sarkin gaisuwar Sallah a ranar laraba. Tawagar Kungiyar Kiristocin ta samu jagorancin shugaban reshan kungiyar dake Kiriu Haruna Ishaya. Da yake Jawabi Mista Ishaya ya bayyana cewa ziyarar wani bangare ne na nuna goyan bayan masarautar tare da yi ma sarkin gaisuawar Sallah. A jawabin Maimartaba Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II ya godewa kungiyar, Inda yai kira da fatan samun zaman lafiya da kunciyar hankali a tsakanin Musulmai da kiristan a fadin kasar.
Sarkin Kano dana Bichi sun jewa Sarkin Musulmi ziyarar Mubaya’a a Sokoto

Sarkin Kano dana Bichi sun jewa Sarkin Musulmi ziyarar Mubaya’a a Sokoto

Siyasa
Me martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da takwaransa na Bichi, Meartaba, Nasir Ado Bayero sun jewa Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ziyarar mubaya'a a Sokoto.   Hakanan Sarakunan sun kuma jewa Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ziyarar Ban Girma a gidan gwamnati. Gwamnan ya bayyana Muhimmancin rawar da masarautar Kano ke takawa wajan zaman Lafiya.
An tsaurara tsaro a Kano saboda fargabar Zanga-zangar Juyin Juya Hali

An tsaurara tsaro a Kano saboda fargabar Zanga-zangar Juyin Juya Hali

Tsaro
An aje jami'an 'yan sanda da na rundunar tsaro na civil defense (NSCDC), a Gadar Lado da shatale-talan Dangi a kan hanyar Zariya da kuma sauran sassan babban birnin jihar tun daga karfe 6:30 na safe. Shugaban yan kungiyar masu zanga-zangar, Omoyele Sowore, wanda ya fitar da wata sanarwa ta shafin shi na twitter, a ranar Talata, ya bayyana Gadar Lado, Titin Zariya a matsayin gurin da za'a gabatar da zanga-zangar ta jihar Kano. Kakakin, Kwamandan Rundunar NSCDC ta Kano, ASC Ibrahim Idris Abdullahi ya tabbatar da cewa wannan aiki ne na hadin gwiwa da aka haddasa sakamakon leken asirin tsaro game da zanga-zangar da wasu kungiyoyin suka shirya gabatarwa. Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wata alamar zanga-zanga a babban birnin jihar yayin da mazauna ke gudanar da harkokinsu na...
Gwamna Ganduje ya ciri tuta inda wata kungiyar Kwararru daga kasar Senegal suka zabeshi a matsayin gwarzon gwamnoni a yaki da Coronavirus/COVID-19 a Najeriya

Gwamna Ganduje ya ciri tuta inda wata kungiyar Kwararru daga kasar Senegal suka zabeshi a matsayin gwarzon gwamnoni a yaki da Coronavirus/COVID-19 a Najeriya

Kiwon Lafiya
Wata Kungiyar kwarru masu saka ido akan lamuran dake faruwa a nahiyar Africa, APREN dake da zama a kasar Senegal ta zabi gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya ciri tuta tsakanin gwamnonin Najeriya a kokarin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.   Kungiyar tace tun kamin a samu mutum na farko da cutar Coronavirus/COVID-19 a Kano gwamnan ya dukufa da daukar matakan ko ta kwana kuma da aka samu mutum na farko haka gwamnan ya yi kokari wajan kula da lamarin. Kungiyar tace saboda jajircewa Gwamna Ganduje yasa har hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta yaba masa da kuma jawo hankalin sauran Mutane su kwaikwayeshi.   Kungiyar tace ta bibiyi duk sauran jihohi inda ta zabi Kano a matsayin gwarzuwar yaki da cutar a kuma ta aikewa da gwamnan s...
Rashin tsaro ya ta’azzara a mazabata>>Alhassan Ado Doguwa

Rashin tsaro ya ta’azzara a mazabata>>Alhassan Ado Doguwa

Siyasa
Dan majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa mazabunshi na Doguwa da Tudun Wada na fuskantar matsalolin tsaro sosai.   Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara Ofishin 'yansandan jihar da kuma barikin sojoji inda yace Dajin Falgore dake makwautaka da Mazabun nashi ya zama guri me hadarin gaske. Ya bayyana cewa lamarin ya kazanta ta yanda ko kusa manoma basa iya zuwa gonakinsu dan fargaba sannan kuma a gida ma mutum bai iya bacci cikin kwanciyar hankali.   Doguwa yace a majalisa zasu yi iya bakin kokarinsu wajan ganin an samarwa da jami'an tsaro kayan aiki.