
Benzema ba zai buga wasan Real Madrid da Barcelona ba
Tauraron dan wasan Real Madrid, Karim Banzema ba zai bugawa kungiyar zakarun gasar La Ligar wasanta na El Classico da Barcelona ba sakamakon raunin dayake fama da shi.
Kocin Madrid, Carlo Ancelotti ne ya tabbatar da hakan inda yace raunin Benzema karami ne amma ba zasuyi wasa da lafiyar tauraron dan wasan su ba.
Madrid zata kara da Barcelona ne da yammacin ranar lahadi inda ta kerewa Barcelona da maki 10 a saman teburin gasar.