fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Karin Kudin Man Fetur

Babu maganar karin kudin man fetur a Watan Maris>>NNPC ta nanata

Babu maganar karin kudin man fetur a Watan Maris>>NNPC ta nanata

Uncategorized
Kamfanin Mai na ƙasa NNPC ya dage kan cewa ba za a yi ƙarin farashin man fetur a wannan watan na Maris ba duk da sanarwar da Hukumar PPPRA mai sa ido kan farashin mai a kasar ta fitar da ke cewa litar mai zai kai Naira 212. NNPC ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter. Da safiyar Juma'a ne Hukumar PPPRA ta fitar da sanarwar da ke cewa farashin mai na iya kai wa Naira 209.61 zuwa Naira 212.6. Amma kawo yanzu sun goge sanarwar daga shafinsu na intanet.
Ku cire Tsammani: Shugaba Buhari ya kawar da yiyuwar dakatar da karin kudin farashin man fetur dana wutar Lantarki

Ku cire Tsammani: Shugaba Buhari ya kawar da yiyuwar dakatar da karin kudin farashin man fetur dana wutar Lantarki

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kawar da yiyuwar dakatar da katin kudin wutar lantarki dana man fetur da aka yi.   Shugaban a jawabin da yayiwa majalisar tarayya a kan kasafin kudin shekarar 2021 ya bayhana muhimmancin karin kudin man dana wutar lantarki inda yace dolene dan tseratar da ayyukan gwamnati. Ya bayyana cewa an mayar da kudin tallafin ne zuwa wasu bangarori da suka fi bukatar kudin. Idan aka yi la'akari da wannan bayani na shugaban kasar to akwai yiyuwar cewa gwamnatin ba zata rage farashin man ko na wutar lantarki ba   “The new petro pricing has freed up resources that were used for subsidy payments, while the new cost-reflective pricing in the electricity industry is meant to address the liquidity challenges in the sector.”
Kace Najeriya na sayar da Mai arha fiye da kasar Saudiyya amma kasan cewa a kasar Saudiyya mafi karancin Albashi Naira Dubu Dari 3 ne?>>Bulama Bukarti ga Buhari

Kace Najeriya na sayar da Mai arha fiye da kasar Saudiyya amma kasan cewa a kasar Saudiyya mafi karancin Albashi Naira Dubu Dari 3 ne?>>Bulama Bukarti ga Buhari

Siyasa
A yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana akan saukin farashin man Fetur a Najeriya idan aka kwatantashi da na sauran kasashe, musamman kasar Saudiyya wadda itace ta daya wajan fitar da man A Duniya, 'yan Najeriya sun fara mayar da martani.   Bulama Bukarti wanda sanannen Lauya ne me ikirarin karw hakkin bil'adama da kuma kokatin tsage gaskiya ya bayyana cewa, shugaba Buhari yace Saudiyyar na sayar da man Fetur da tsada fiye da Najeriya amma kuma ya sani mafi karancin Albashi a Saudiyya kwatankwacin Naira 305,000 ne wanda ya kama Riyal 3,000.   Ya kara da cewa ka biyamu irin wancan Albashin, muma zamu biya Naira 168 a matsayin kudi  man fetur na kowace lita, kamar kasar Saudiyya. https://twitter.com/bulamabukarti/status/1311566853614063616?s=19 ...
Yajin aikin da kuke niyyar shiga zai kara yawan matsalar tattalin arziki ne>>Gwamnoni ga kungiyar Kwadago

Yajin aikin da kuke niyyar shiga zai kara yawan matsalar tattalin arziki ne>>Gwamnoni ga kungiyar Kwadago

Siyasa
Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta jawo hankalin kungiyar kwadago kan cewa yajin aikin da take son shigaba a ranar Litinin me zuwa zai kara saka Najeriya cikin matsin tattalin arziki ne.   Hakan na fitowa ne daga mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin, Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal. Ya bayyana cewa, Yajin aikin zai kara jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki ne bayan wanda Coronavirus/COVID-19 ta sakata, yace ya kamata kungiyoyin kwadagon su fahimci cewa Tallafin man na kara matsalar rashawa da cin hanci ne.   Kungiyar tace ta wakilta wasu daga cikin membobinta dan shiga tsakanin Gwamnati da kungiyar kwadagon kan wannan lamari.
Kungiyar kwadago ta baiwa Gwamnati sati 2 ta janye karin kudin mai dana wutar lantarki ko su fara zanga-zanga

Kungiyar kwadago ta baiwa Gwamnati sati 2 ta janye karin kudin mai dana wutar lantarki ko su fara zanga-zanga

Siyasa
Kungiyar kwadago ta NLC bayan zaman da ta yi na masu ruwa da tsaki jiya, Laraba, ta fitar da sanarwar cewa ta baiwa gwamnati mako 2 dan ta janye karin kudin wutar lantarki dana Man Fetur da ta yi ko kuma ta fuskanci zanga-zanga. Shugaban kungiyar, Ayuba Wabba ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai inda yace nan da 28 ga watan Satumba idan gwamnati bata janye karin kudin wutar dana Man Fetur da ta yi ba to zasu fara Zanga-zanga.
Karin Kudin Mai: Zaman tattaunawa tsakanin Gwamnati da kungiyoyin Kwadago bai samu nasara ba, Sun ce yajin aiki babu ja da baya

Karin Kudin Mai: Zaman tattaunawa tsakanin Gwamnati da kungiyoyin Kwadago bai samu nasara ba, Sun ce yajin aiki babu ja da baya

Siyasa
Zaman da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin Kwadago na Najeriya ya kare baram-baran ba tare da samun matsayaba.   A zaman da aka yi jiya, gwamnati ta gabatar da tsare-tsaren da take dashi sannan ta gayawa kungiyoyin kwadagon cewa, ba zata uya ci gaba da bada tallafin mai ba. Saidai kungiyoyin kwadagon sun yi watsi da hujjojin gwamnati inda suka bayyana cewa, ba zasu amince da wani Uzuri ba in banda janye karin kudin man fetur din dana wutar Lantarki.   Saidai Punch ta ruwaito cewa, Kungiyoyin Kwadagon zasu koma su zauna da masu ruwa da tsaki dan tattauna abubuwan da Gwamnatin ta gaya musu sannan su sake zama da ita.  
Karin Kudin Mai:Idan kuka sake kuka fito zanga-zanga zaku dandana kudarku>>’Yansanda suka gargadi Kungiyar Daliban Najeriya

Karin Kudin Mai:Idan kuka sake kuka fito zanga-zanga zaku dandana kudarku>>’Yansanda suka gargadi Kungiyar Daliban Najeriya

Tsaro
'Yansanda a jihar Ogun sun gargadi kungiyar Daliban Najeriya ta NANS cewa kada su sake su aiwatar da zanga-zanga akan karin kudin man fetur dana wutar Lantarki da suka shirya yi ranar Litinin me zuwa.   Sanarwar ta fitone daga kakakin hukumar 'yansandan jihar, Abimbola Oyeyemi inda yace sun samu bayanin cewa daliban zasu fito su tare manyan hanyoyin jihar. Yace hukuma ba zata zira ido wasu tsiraru saboda kawai san ransu da jin dadinsu su kadai su hana sauran al'umma walwala ba, dan haka suna baiwa kungiyar daliban shawarar su janye wannan zanga-zanga dan bata cikin doka.   Yace an baiwa 'yansanda umarnin zama cikin shirin ko ta kwana akan wannan lamari dan haka yana baiwa iyaye shawarar kada su bar 'ya'yansu su fito wannan zanga-zanga inda ya karkare da cewa id...
Kana Musgunawa ‘yan Najeriya kuma babu wani Tarihin da zai tuna da kai>>PDP tawa shugaba Buhari martani

Kana Musgunawa ‘yan Najeriya kuma babu wani Tarihin da zai tuna da kai>>PDP tawa shugaba Buhari martani

Uncategorized
Jam'iyyar Hamayya ta PDP ta bayyana cewa karin kudin man da aka yi na muzgunawa 'yan Najeriya ne kawai.   Tana martanine akan maganar da shugaba Buhari yayi kan karin kudin man inda tace har yana da bakin da zai kare karin kudin man da wanda ya gada daga PDP akan Naira 87 kan kowace Lita amma ya mayar dashi Naira 160? PDP da take magana da ta bakin sakataren watsa labaranta, Kola Ologbondiyan,  ta bayyana cewa a daina kwatanta farashin mai a Najeriya da sauran wasu kasashe wanda sun fi Najeriya karfin tattalin Arziki sannan kasashen su basa cikin matsin rayuwa.   PDP tace duk da 'yan Najeriya sun yi Allah wadai da karin kudin man amma shugaban ya nuna ko a jikinsa. Tace tarihi ba zai wani tuna da shugaban da baiwa mutane Adalci ba.