
Nazir Ahmad ya samu karuwa”idan namijine a sakamai Buhari, idan macece a sakamata Buhariyya”
Tauraron mawakin hausa, Nazir Ahmad, Sarkin waka ya samu karuwar diya mace, Muna tayashi murna da fatan Allah ya rayata rayuwa me albarka, abokin aikinshi Nazifi Asnanic ya tayashi murna sannan yace yana neman alfarmar idan namijine a sakamishi Buhari idan kuma macece a sakamata Buhariyya.
Saidai Nazir ya mayarwa da Nazifi amsar cewa dadai namijinne da zai iya saka mishi buhari, amma buhariyya tutafa kenan.