fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Karya

An kama wani mutum da buga takardar mutuwar mahaifinshi ta Karya

An kama wani mutum da buga takardar mutuwar mahaifinshi ta Karya

Tsaro
Jami'an 'yansanda a babban birnin tarayya,Abuja sun kama wani mutum me suna Success Desmond dan kimanin shekaru 38 wanda Injiniya ne da laifin buga takardar karya ta mutuwar mahaifinsa.   Mutumin ya kjma yi karyar cewa shine magajin mahaifin nashi inda yayi amfani da wannan takardar karya wajan Farfado da layin wayar MTN na mahaifin nashi. Mutumin ya gurfana a gaban Kotun Majistre Wuse Zone 6 dake babban birnin tarayya, Abuja. Saidai da aka karanto mai laifinshi yaki amsawa.   Lauyanshi ya nemi a bada belinshi,kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito kuma mai shari'a, Ahmed Ndajiwo ya amince inda ya bada belinshi akan Naira Dubu Dari 5 da kuma mutane 2 da zasu tsaya mai wanda dole ya kasance suna cikin Abuja.