fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Tag: Kasar Chadi

Ya kamata a gayyatato sojojin kasar Chadi tunda sun iya yaki da Boko Haram>>Gwamna Sule ya baiwa Buhari shawara

Ya kamata a gayyatato sojojin kasar Chadi tunda sun iya yaki da Boko Haram>>Gwamna Sule ya baiwa Buhari shawara

Tsaro
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa, yana goyon bayan gayyato sojojin haya akan maganin matsalar tsaro.   Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channelstv inda yace an ga yanda Sojojin kasar Chadi suka yi yaki da Boko Haram kuma suka yi galaba akansu. Yace idan aka gayyato su dan taimakawa wajan magance matsalar a Najeriya abune me kyau
‘Yan Boko Haram fiye da dubu 1 sun mutu a gumurzu da Chadi

‘Yan Boko Haram fiye da dubu 1 sun mutu a gumurzu da Chadi

Siyasa
Gwamnatin Chadi ta fitar da alkaluman da ke cewa dakarunta 52 ne suka rasa rayukansu yayin da mayakan Boko Haram sama da dubu daya suka hallaka a fadan da aka share tsawon kwanaki ana gwabzawa tsakanin bangarorin biyu a zagayen tafkin Chadi.     Kakakin Rundunar Sojin kasar, kanar Azem Bermendoa Agouna, ya ce baya ga kashe mayakan na Boko Haram sama da dubu daya, an kuma lalata babura da kuma kananan jiragen ruwan da ‘yan ta’addar ke amfani da su don kai farmaki.     Wannan ne dai karon farko da rundunar sojin kasar ta Chadi ta sanar da yawan dakarunta da suka mutu bayan kaddamar da farmaki kan mayakan na Boko Haram da ta yi wa take da 'fushin Bohoma.'
Ka Tuba ka ajiye makamanka ko in Hallakaka>>Shugaban Chadi ga Shekau

Ka Tuba ka ajiye makamanka ko in Hallakaka>>Shugaban Chadi ga Shekau

Siyasa
Shugaban Chadi, Idriss Deby ya bukaci shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da ya mika kansa ko kuma ya kashe shi a mabuyarsa da ke Dikwa.     Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan da shugaba Deby ya jagoranci dakarunsa wajen kaddamar da farmaki kan mayakan Boko Haram tare da kashe mutun 100 daga cikinsu.     A yayin jawabi ga al’ummar Chadi ta kafar talabijin, shugaba Deby ya ce, Shekau na da damar mika wuya a yanzu, in ba haka kuma, a yi amfani da wuta wajen fatattako shi daga mabuyarsa.     Deby ya gargadi Shekau cewa, zai aika shi lahira muddin ya ki mika wuya kamar yadda aka bukace shi ya yi. A makon jiya ne, dakarun Chadi suka kaddamar da farmaki kan mayakan Boko Haram, farmakin da aka yi wa lakabi da 'fushin Boma'...
Shekau yawa Shugaban kasar Chadi Barazana a sabon Bidiyo

Shekau yawa Shugaban kasar Chadi Barazana a sabon Bidiyo

Siyasa
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya mayar da martani ta sautin murya kan harin da kasar Chadi ta kaiwa mayakansa.   Sakon me tsawon mintuna 5 da jaridar Thenation ta samu an ji Shekau na fadin cewa Idris Derby na cikin matsala tunda ya taba Allah.   A cikin Sakon Shekau yace kisan da sukawa sojojin Chadi Allah ne ya basu nasara kuma duk abinda Idris Derby din zai musu to ba zai yi Nasara a kansu ba.   Shekau yayi kira ga mayakanshi da kasa du gudu su jajirce dan irin wannan abu ya faru a baya kuma tunda suna tare da Allah to zasu yi Nasara.   Ya kuma yi kira ga jama'ar kasar Chadi da su tashi tsaye domin irin rayuwar da suke ba bisa shari'a take ba, yace idan kuma sun kiya to Allah zai basu Nasara.
Hotuna: Shugaban Kasar Chadi ya kaiwa sojojin kasar da suka jikkata dalilin yaki da Boko Haram ziyara

Hotuna: Shugaban Kasar Chadi ya kaiwa sojojin kasar da suka jikkata dalilin yaki da Boko Haram ziyara

Siyasa
Shugaban kasar Chadi,Idris Derby ya kaiwa sojojin kasar da suka jikkata dalilin batakashin da suka yi da Boko Haram ziyara inda ya basu karfin gwiwa. Shugaban ya jagoranci sojojinshi zuwa yankin tafkin Chadi inda sansanin  Boko Haram yake suka kuma tashesu. Rahotanni da dama sun bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun kwarara zuwa cikin Najeriya dan Neman mafaka.