fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Kasar Mali

Yanzu-Yanzu:Ciwon mutuwar barin jiki ya kama hambararren shugaban kasar Mali

Yanzu-Yanzu:Ciwon mutuwar barin jiki ya kama hambararren shugaban kasar Mali

Siyasa, Uncategorized
Rahotanni daga kasar Mali na cewa ciwon mutuwar rabin jiki ta kama hambararren shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita.   Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa likitan Shugaban ya gaya musu ciwon ba mai tsanani bane amma alamace dake nuna cewa nan gaba me tsananin zai iya kama shugaban. A baya dai wani hadimin shugaban ya bayyana cewa an kwantar dashi a Asibiti kuma za'a sallameshi a yau dan kawai ya je a duba lafiyarsa ne amma daga baya kuma sai aka bayyana cewa za'a ci gaba da dubashi har abinda hali yayi.   Sojojin da suka hambarar dashi dai sun bayyana cewa idan akwai bukatar ya fita kasar waje neman lafiya zasu bashi damar hakan.
Ni tun tuni na hango cewa za’a wa kasar Mali juyin Mulki>>Fasto Ayodele

Ni tun tuni na hango cewa za’a wa kasar Mali juyin Mulki>>Fasto Ayodele

Siyasa
Fasto Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual ya bayyana cewa tuni ya hango cewa za'a wa shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita juyin mulki.   A sanarwar da ya aikewa da Daily Post, Faston ya bayyana cewa tun a watan Disamba na shekarar 2019 ya gayawa manema labarai cewa hakan zata faru inda kuma yayi gargadi. Hutudole ya ruwaito muku yanda sojoji a kasar Mali suka kama shugaban kasar Ibrahim Boubacar  Keita bayan kamen shugaban ya bayyana cewa Yayi Murabus saboda baya son a zubar da jini saboda shi.