fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Kashim Shattima

Zulum Ya Fi Ni, Ta Kowane Fanni>>Tshohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima

Zulum Ya Fi Ni, Ta Kowane Fanni>>Tshohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima

Siyasa
Sanata Kashim Shettima mai wakiltar Borno ta Tsakiya a Majalisar Dokoki ta kasa ya tabbatar da cewa zabar Gwamna Babagana Zulum a matsayin wanda zai gaje shi ba don wasu dalilai na kashin kansa ba amma don maslahar jihar ta Borno ne. Ya yi nuni da cewa Farfesa Zulum 'ya fi shi a duk wasu bangarori.' Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wata makala a wajen taron laccar Jama'a da Hadin gwiwar Kungiyoyin Matasa suka shirya a Birnin Kebbi tare da taken: "Cigaban Matasa da Jagoranci." Ya bayyana cewa ya tsallake matsaloli da yawa har ya kai ga ya zabi wanda zai gaje shi, Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda kuma ya bayyana a matsayin amintaccen dan siyasa. Tsohon Gwamnan ya shawarci shuwagabanni da su fahimci cewa shugabanci ya kasance ama...