
Gwamnatin jihar Katsina tasha al’washin samar da cibiyoyin killace masu cutar coronavirus a fadin jihar
Gwamnatin jihar Katsina ta ce tana gina cibiyoyin keɓewa, tare da yunkurin samar da gadaje guda 722, a duk faɗin jihar don inganta kula da marassa lafiyar dake fama da cutar COVID-19.
Gwamna Aminu Masari ya sanar da haka lokacin da ya amshi motocin daukar marasa lafiya guda uku, wanda gidauniyar BUA ta bayar a jihar, ranar Alhamis a cikin garin Katsina.
A cewar sa “Mu da kanmu muna gina cibiyoyin keɓewa a wurare daban-daban a fadin jihar, tare da yunkurin samar da gadajan kwanciya guda 722, don kula da marasa lafiya dake fama da cutar Coronavirus.
Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa an gama gina cibiyar killacewa guda daya a jihar.
Shima dai A ta bakin Shugaban Gidauniyar na BUA, Alhaji Abdussamad Ishaq Rabiu, ya ce an ba da motocin guda uku don inganta har...