
An kashe jami’an tsaro tare da wasu yan gari Mutum Shida a sabon harin da ‘yan bindiga suka kai a wasu kauyuka dake jihar Katsina
Wani Jami'in tsaro da wasu mutane 6 sun rasa ransu a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai a wasu kauyuka dake jihar Katsina kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito
An dai kashe jami’an tsaron ne tare da wasu yan gari mutum shida da sanyin safiyar ranar Alhamis a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane uku a cikin kauyukan kanga da kanawa.
An kuma bayyana cewa wani jami’in tsaro ya rasa ransa lokacin da ‘yan bindigar suka yi wani kwanton bauna lokacin da suke aikin ceto a kauyukan.
Yawancin mazauna wurin sunji rauni yayinda harin ya rutsa da wasu mata masu dauke da juna biyu a babban asbitin Danmusa.
Da yake tabbatar da harin, kakakin rundunar ‘...