
Rundunar Sojin Najeriya tayi Nasarar cafke ‘yan bindiga158 A Jahohin Katsina, da Zamfara
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Sahel Sanity sun kama wasu 'yan bindiga 158 a kokarin da rundunar ta ke na kawar da ayyukan 'yan bindigar a jihohin Katsina da Zamfara.
Birgediya janar Bernard Onyeuko, Mataimakin Daraktan Watsa Labarai na Rundunar, Operation Sahel Sanity, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a sansanin Sojoji na musamman da ke Faskari ranar Talata.
Onyeuko ya bayyana cewa sojojin da ke aiki da bayanan sirri, sun kai farmaki wani yanki a karamar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, inda suka kama 'yan bindiga 150 tare da kwace bindigogi 120.
Ya ce, sojojin sun kuma sake kai farmaki wani sansanin 'yan bindiga a karamar hukumar Anka da ke Zamfara, inda aka kame wasu masu garkuwa da mutane biyu yayin da aka kwato bindiga kirar AK 47 guda ...