fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Kauran Namoda

Da Duminsa:Ana Zargin wani DPO da hada baki da ‘yan Bindiga a Zamfara, Ji Matakin da hukumar ‘yansanda ta dauka akansa

Da Duminsa:Ana Zargin wani DPO da hada baki da ‘yan Bindiga a Zamfara, Ji Matakin da hukumar ‘yansanda ta dauka akansa

Tsaro
Hukumar 'yansandan Najeriya ta dauki mataki akan DPO na garin Kauran Namoda dake jihar Zamfara saboda zarginsa da hannu wajan hada baki da 'yan Bindiga masu kaiwa jama'a hari.   Kakakin 'yansandan Jihar, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar Lamarin inda yace sun ga Bidiyon dake ta yawo a shafukan sada zumunta ana zargin DPO na Kauran Namoda da hada kai da 'yan Bindiga.   Yace a yanzu dai babu wani korafi a hukumance da aka shigar akan DPO din amma duk da haka, Kwamishinan 'yansansan jihar, Abutu Yaro ya canja masa wurin aiki. Yayi kira ga Jama'ar gari, duk wanda ke da shaidar cewa DPO din na da hannu a wajan taimakawa 'yan Bindiga to ya kawowa hukumar.   Ya kuma ce a matsayinsa na jami'in Doka, DPO din na da damar shiga tsakani, tsakanin Fulani da Hausa...
Sarkin Ƙauran Namoda ya rasu

Sarkin Ƙauran Namoda ya rasu

Uncategorized
  Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda a jihar Zamfara Alh. Muhammad Ahmad Asha rasuwa bayan shekara 16 a gadon sarauta.     Sarkin ya rasu ne da safiyar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda wani na kusa da fadar Ƙaura Namoda ya tabbatar wa BBC.     Amma Sarkin ya dade yana fama da hawan jini da kuma ciwon suga.     Babu dai wani cikakken bayani kan dalilin rasuwarsa.   Shi ne Sarki na biyu a tarihin sarautar Sarki mai sanda ta Emir mai daraja ta ɗaya a Ƙauran Namoda bayan mahaifinsa, amma shi ne Sarki na 16 a masarautar Kiyawan Ƙauran Namoda.     Sarkin ya rasu yana da shekara 71 a duniya, kuma ya bar mata uku da ƴaƴa.