fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Kenya

An kama dan Najeriya, Bala Ma’azu a kasar Kenya da Kudade Makare a jikarsa

An kama dan Najeriya, Bala Ma’azu a kasar Kenya da Kudade Makare a jikarsa

Tsaro, Uncategorized
An kama wani dan Najeriya a kasar Kenya, me Suna Bala Ma'azu da kudade makare a cikin jakarsa. Akwai Dalar Amurka da Euros da kuma Naira.   An kamashine a filin jirgin saman kasar me suna Jomo Kenyatta.  An gano Dala 880,000 da Euros 60,000 sai kuma takardun Naira na 63,000.   An kamashine yana kokarin hawa jirgi zuwa Dubai inda ake wa kallon birnin da aka fi kai kudaden sata a Duniya. Ranar 4 ga watan Disamba ne ya bar Legas zuwa kasar Kenya. An bayyana kama Bala sabods ya kasa nuna takardun da suka bashi izinin daukar irin wadancan makudan kudade. Amma ya nace akan cewa kudin na Halal ne.
Annobar kwalara ta barke inda ta kashe mutane 13

Annobar kwalara ta barke inda ta kashe mutane 13

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga kasar Kenya na cewa mutane 13 ne suka rasa rayukansu sandin annobar cutar Coronavirus/COVID-19 data barke a kasar biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi. Sakataren Lafiya na Kasar, Mutahi Kagwe ya bayyana cewa akalla mutane 550 ne suka kamu da cutar a Arewacin kasar.   Sanarwar daya fitar jiya, Alhamis kamar yanda NAN ya ruwaito yace an samu matalar ne a garuruwan Marsabit da Turkana, saidai yace jami'an lafiya na iya bakin kokarinsu dan shawo kan lamarin.   Cutar Amai da gudawa dai na samuwa dalilin gurbataccen ruwan sha ko kuma abinci wanda idan ta yi muni takan kai ga rasa rai.
Hotuna: ‘Yan Sanda A kasar Kenya sun kama Mutumin da yayi amfani da Gam ya rufe Al’aurar Matarsa

Hotuna: ‘Yan Sanda A kasar Kenya sun kama Mutumin da yayi amfani da Gam ya rufe Al’aurar Matarsa

Auratayya
'Yansanda a kasar Kenya sun bayyana nasarar kama wani magidanci me kimanin shekaru 30 da yayi Mafani da Sufa Gulu ya rufe al'aurar matarsa.   James Kifo Muruiki ya aikata wannan laifine a Ranar 16 ga watan Mayu saidai bayan da matar tasa ta kai kara wajan 'yansanda sai ya shiga buya. Hukumar dake binciken mayan laifuka ta kasar Kenya ta bayyana cewa, a karshe dai an kama mutumin kuma bayan kammala bincike za'a gurfanar dashi a gaban kuliya.   Tace yanda ya aikata laifin shine, ya ja matarsa can bayan gari cikin dare inda ya sakata ta yi tsirara sannan ya fara tambayarta maza nawa ta yi lalata dasu lokacin baya nan? Da taki gaya masa shine ya mata dukan kawo wuka, ya saka mata yaji, Gishiri da gam din super Gulu a al'aurarta inda yayi amfani da wuka ya tu...
Hotuna:An kama Mataimakin Gwamnan daya karya dokar killacewa ta Coronavirus/COVID-19

Hotuna:An kama Mataimakin Gwamnan daya karya dokar killacewa ta Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Mataimakin gwamnan jihar Kilifi dake kasar Kenya, Gideon Saburi ya gamu da fushin Hukuma bayan da aka kamashi da karya dokar killace kai dan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   Rahotanni daga kasar sun bayyana cewa mataimakin gwamnan ya rika halartar tarukan biki dana jana'iza sannan kuma ya rika mu'amala da ma'aikatansa kai gadi duk da cewa bai dade da dawowa daga kasar Jamus ba. Kasar Kenya na da dokar mutum ya killace kansa na tsawon kwanaki 14 bayan dawowa daga daya daga cikin kasashen dake fama da cutar Coronavirus/COVID-19 amma shi gwamnan bai yi hakan ba.   Shugaban 'yansandan yankin ya bayyana cewa, suna tatsar bayanai daga wajan mataimakin gwamnan da suka hada da ko da gangan yake wannan abu kuma yaya maganar killace kanshi da bai yi ba. ...