
Ku daina aikomin da sakon Innalillahi wa inna ilaihi raji’un bamu mutu ba>>Diyar Sarki Sanusi
Diyar Sarkin Kano da gwamnatin jihar ta sauke daga Sarauta, Muhammad Sanusi, watau Khadija Sanusi ta caccaki masu aike mata da sakon kalmar Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un bayan sauke mahaifin nata daga Sarauta.
A wani sako data saki a Shafinta na Twitter wanda daga baya ta goge amma Jaridar Punch ta sameshi.
Khadija ta rubuta cewa, Dan Allah ku daina aikomin Sakon Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, dan bamu mutu ba.
Ta yi fatan Cewa Allah yasa abinda ya faru hakan ya zama mafi Alheri.