fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Kidaya

Buhari ya amince da Naira biliyan 10 domin yin kidaya

Buhari ya amince da Naira biliyan 10 domin yin kidaya

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sakin naira biliyan 10 ga hukumar kidaya ta kasa (NPC) domin ci gaba da shata kan iyakokin yankin (EAD) a sauran ragowar kananan hukumomin 546 na kasar. Har ila yau, Buhari ya amince da karin naira biliyan N4.5 don sanya shi a cikin Kasafin Kudin na 2021 don kammala aikin a matsayin wani bangare na shirye-shiryen kidayar da za a yi. Shugaban riko na NPC, Dr. Eyitayo Oyetunji, ya bayyana wadannan ne a Abuja yayin da yake yi wa manema labarai bayani game da sakin kudaden da kuma sabuntawa kan EAD a hedikwatar NPC.