
Shugaba Buhari ba zai iya baiwa ‘yan Najeriya kariya ba>>Kingsley Moghalu
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Kingsley Moghalu ya bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai iya baiwa 'yan Najeriya kariya ba amma kuma yana takurawa masu zanga-zangar lumana.
Moghalu na maganane akan kisan mutane 43 da aka yi a Borno inda yace abin kunyane ga 'yan ta'adda an kasa maganinsu sai masu zanga-zangar lumana ake takurawa.
Yayi Allah wadai da lamarin inda kuma ya bayyana cewa a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Najeriya na kara durkushewa.
“The barbaric beheading of 43 Nigerians in Zabarmari village in Borno State by Boko Haram is a national outrage and tragedy. It’s increasingly clear that @NigeriaGov is unable to protect the lives of Nigerians. What does that mean? Our country is becoming a failed state.
...