
Yanzu Mun shirya a kawo mana rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19>>Jihar Kogi
Jihar Kogi ce daya tilo cikin jihohin Najeriya da ba'a kaiwa rigakafin Coronavirus/COVID-19 ba. Saidai a yanzu ta bayyana cewa ta shirya karbar Rigakafin.
Hakan ya fito ne daga kwamishinan yada labaran jihar, Kingsley Fanwo wanda ya bayyanawa Independent.
Yace ba gaskiya bane wai sun ce ba zasu karbi rigakafin Coronavirus/COVID-19 ba, yace sun fada tun a baya cewa a yayin zanga-zangar SARS ne aka lalata inda ya kamata ace sun ajiye rigakafin amma suna kan gyaranshi.
Yace a yanzu sun kammala gyaran kuma sun sanar da gwamnatin tarayya cewa zaa iya kawo mudu rigakafin.
“There was no time that the governor said he would not accept the COVID-19 vaccine. He told the entire world on television and in conferences that he was ready to accept the COVID-1...