
Bidiyon mawaki, Korede Bello tsaye a gaban shugaban ‘yansanda yana gaya masa ya hana ‘yansanda harbin masu zanga-zanga
A jiya ne dai shugaban 'yansandan Najeriya, IGP, Muhammadu Buhari ya gana da matasan mawakan kudancin Najeriya akan zanga-zangar SARS.
Daga cikin wanda ganawarsa da shugaban 'yansandan ta fito Fili shine Davido wanda aka zargeshi da nesanta kansa da masu zanga-zangar duk da ya karyata hakan.
A yanzu kuwa bidiyin mawaki Korede Bello ne ya bayyana inda aka ganshi shima a ganawar da akayi da shugaban 'yansandan yana rokonsa cewa dan Allah ya baiwa yaransa umarnin su daina harbin masu zanga-zanga.