fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Koriya ta Arewa

Kasar Koriya ta Arewa ta kashe wani dan kasarta da ya karya dokar kullen Coronavirus/COVID-19

Kasar Koriya ta Arewa ta kashe wani dan kasarta da ya karya dokar kullen Coronavirus/COVID-19

Tsaro
Kasar Koriya ta Arewa ta kashe wani da kasarta a bainar jama'a saboda karya dokar kullen Coronavirus/COVID-19.   Kafar RFA ta bayyana cewa an kashe wanda ya karya dokar ne bayan samunsa da laifin Fasa kwauri da wani abokinsa dan kasar China.   Sannan an yake wannan hukunci ne a bainar jama'a dan saka fargaba ga duk wanda zai yi tunanin yin irin wannan laifi nan gaba. Kasar ta Koriya ta Arewa na ikirarin cewa bata da cutar Coronavirus/COVID-19 amma ta saka dokar hana zirga-zirga musamman tsakaninta da kasashe makwauta.
Kasar Koriya ta Arewa ta kashe dan kasar Koriya ta kudu da kuma kona gawarsa

Kasar Koriya ta Arewa ta kashe dan kasar Koriya ta kudu da kuma kona gawarsa

Siyasa
Rahota ni daga kasar Koriya ta kudu na cewa hukumomin kasar na zargin makwabciyarta, Koriya ta Arewa da kashe mata wani mutum sannan ta kona gawarsa.   Yonhap ta ruwaito cewa kasar Koriya ta Kudu taga gawar mutumin a cikin ruwanta ne inda an kone ta. Dan hakane kasar ta Bukaci Koriya ta Arewa data hukunta wanda suka yi wannan aika-aika. Tace kuma tana bukatar a mata bayanin dalilin kisan. Mutumin dan kimanin shekaru 47 dake aiki da wani ma'aikatar kamin kifi da kula da tekun kasar ya bacene yayin da yake ran gadin ruwan.   An bazama nemansa amma ba'a ganshi ba sai gawarsa ta bayyana daga abaya a kone.
Shugaban kasar Koriya ta Arewa na cikin Mawuyaci Hali: Yana shirin Mikawa kanwarsa Ragamar kasar>>Inji Makwauciya, Koriya ta Kudu

Shugaban kasar Koriya ta Arewa na cikin Mawuyaci Hali: Yana shirin Mikawa kanwarsa Ragamar kasar>>Inji Makwauciya, Koriya ta Kudu

Siyasa
Rahotanni daga Koriya ta Kudu na cewa shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un na cikin wani Mawuyacin hali inda yake kokarin baiwa kanwarsa, Kim Yo Jong ragamar mulkin kasar.   Tsohon Hadimin tsohon shugaban kasar Koriya ta Kudu, Chang Song Min ya bayyanawa Manema labarai cewa shugaban na koriya ta Arewa na cikin halin ni 'yasu amma kasar nata kumbiya-kumbiya. Yace an riga an shirya baiwa kanwarsa ragamar milkar kasar dan ba za'a bar kasar ba shugaba ba.   A baya dai kasar Koriya ta Arewa ta saki wasu hotuna na shugaban kasar yana wani taro amma kamfanin dillancin labarai na Reuters yace babu tabbacin sahihancin wadannan hotuna.   A farkon shekarar nan aka yi ta yada cewa shugaban ka Koriya ta Arewa ya Mutu saboda aiki da aka masa wanda bai yi na...
Kasar Koriya ta Arewa ta mallaki makaman kare Dangi 60

Kasar Koriya ta Arewa ta mallaki makaman kare Dangi 60

Tsaro
Rahotanni daga Hukumar sojojin kasar Amurka na cewa kasar Koriya ta Arewa ta mallaki makaman kare dangi da suka kai 60.   Hakanan kuma kasar ta Mallaki makamai Masu guba da suka kai Dubu 5. Hutudole ya samo muku daga Daily Star yanda sanarwar da sojojin Amurjar suka fitar ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar yawan makaman kasar ta Koriya ta Arewa sukai 100 nan da karshen shekarar nan da muke ciki. Sannan kasar na shirin kaddamar da harin makami me guba akan kasar Koriya ta Kudu. Kadar Koriya ta Kudu ta tabbatar da wannan lamari. An dai gano cewa kasarce ta 3 a Duniya wajan samun makamashin hada makami me guba.   Sannan tana da wasu kwararrun masu satar bayanai da kutse a Kwamfuta dubu 6 dake aiki a kasashen Duniya daban-daban dan tattara mata da bayanan sirri.
Da Dumi-Dumi: An yi musayar wuta tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta kudu da safiyar yau

Da Dumi-Dumi: An yi musayar wuta tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta kudu da safiyar yau

Siyasa
Rahotanni daga kasar Koriya ta Kudu na cewa bayan bayyanar shugaban kasar Koriya ta Arewa a bainar jama'a  jiya,bayan da ya kwashs kusan mako 3 ba'a ganshi ba abinda ya jawo aka rika cewa ya mutu, kasar ta Koriya ta Arewa ta yi takalar fada.   A wani mataki da ake ganin na nuna cewa har yanzu shugaban Koriya ta Arewar, Kim Jong Un na nan da rai kuma shine ke jan ragamar mulkin kasar, sojojin koriya ta Arewar sun yi barin albarusai a iyakar koriya ta Kudu.   Hakan yasa itama koriya ta Kudu bata yi wata-wata ba ta mayar da martanin ruwan Albarusai cikin Koriya ta Arewar, kamar yanda Daily Mail ta ruwaito.   Saidai sanarwar da Koriya ta kudun ta fitar ta bayyana cewa bata tunanin da ganganne aka yi harbin.   Sannan kuma sanarwar ta bayyana cewa ...
Shugaban kasar Koriya ta Arewa na nan da Ransa>>Cewar Mahukuntan Koriya ta Kudu

Shugaban kasar Koriya ta Arewa na nan da Ransa>>Cewar Mahukuntan Koriya ta Kudu

Siyasa
A jiyane dai aka samu Rahotanni daga TMZ na kasar Amurka da HKSTV na Hongkong cewa shugaban Koriya ta Arewa,Kim Jong Un ya mutu bayan wani aiki da aka masa a zuciya da bai yi daidai ba.   Saidai Sabon Rahoton Daily Mail da Daily Star na cewa mahukuntan makwauciyar Koriya ta Arewa,watau Kasar Koriya ta kudu sun tabbatar da cewa Jong Un nanan da ransa, ya je hutune.   Chung-in Moon wanda shine me baiwa shugaban kasar Koriya ta Kudu shawara kan harkokin kasashen waje ya bayyana cewa Jong Un yana can wani gefe ne na kasar Koriya ta Arewa yana hutawa.   Ya gayawa Foxnews cewa matsayarsu dayace, Shugaban Koriya ta Arewa na nan da ransa bai mutu ba kuma lafiyarsa qalau.   Ya kaa da cewa tun a ranar 13 ga watan Afrilunnan Jong Un ke can wani gefen ka...