fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Koriya

Yan kasar Koriya ta Arewa na Guna-Guni saboda Gwamnati tace kowa ya kawo karensa a yanka a ci saboda karancin abinci a kasar

Yan kasar Koriya ta Arewa na Guna-Guni saboda Gwamnati tace kowa ya kawo karensa a yanka a ci saboda karancin abinci a kasar

Uncategorized
Hukumomi a kasar Koriya ta Arewa sun bukaci masu karnuka a gidaje su bayar dasu a yanka a ci.   Kasar ta haramata ajiye Karnuka a yanzu inda ake kaisu gidajen Abinci ana yankawa wasu kuma da suka yi rara ana kaisu gidan ajiyar Dabbobi. Shugaban kasar, Kim Jong Un ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda karancin Abinci da ya afkawa kasar. Hutudole ya samo muku cewa yawanci masu kudi ne ke ajiye karnuka a kasar amma talakawa suna kiwon Aladene da sauran dabbobi.   Rahoton Sky News ya bayyana cewa, masu kudi a kasar nata gunaguni amma babu abinda zasu iyayi.