
Jami’an Gwamnati 6 a Najeriya da a baya suka yanke jiki suka fadi a Kotu
Yadda jami'an gwamnati ke yanke jiki ko nuna halayya ta rashin lafiya a lokacin da ake bincikarsu, ba sabon abu ba ne a Najeriya.
An sha ganin ƴan siyasa ko wasu masu riƙe da muƙami na sumewa a kotu, wasu kuma na halartar kotun saman gadon asibiti ko keken guragu da nufin neman afuwa ko sassauci a shari'ar da ake masu.
Yawancinsu ana zarginsu ne da wawushe dukiyar ƙasa ko kuma almundahana.
Mun yi nazari kan jami'an gwamnati shida a Najeriya da suka yanke jiki suka faɗi a kotu ko suka halayya ta rashin lafiya.
Abdulrasheed Maina
Tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina wanda ake shari'arsa tun 2019 ya yanke jiki ya faɗi a kotun Abuja bayan sake bayyana gaban kotun a ranar Alhamis
Maina ya yanke ji...