fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Kudiddifi

Yaro dan shekara 13 ya mutu a wani kududdufi a jihar Kano

Uncategorized
Wani yaro dan shekaru 13, Abdullahi Musa, ya nitse yayin da yake wanka a wani kududufi da ke kauyen Dangayaki a karamar hukumar Karaye ta jihar Kano. A wata sanarwa da Alhaji Saidu Muhammed, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ya sanar da haka a ranar Laraba. Muhammed ya ce lamarin ya faru ne a ranar 30 ga Satumba, 2020. “Mun samu kiran waya daga Malam Adamu Muhammad da misalin karfe 10:45 na safe. “Da samun labarin, muka hanzarta tura jami’anmu na ceto zuwa wurin da misalin karfe 11:00 na safe. "An mika gawar Musa ga Shugabanmu da ke kauyen Dangayaki, Alhaji Abdulmuminu." Muhammed ya kara da cewa musabbabin faruwar lamarin ana kan gudanar da bincike.