
Coronavirus/COVID-19 ta kashe likita a Kaduna
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ta kashe Likita, Dr. Clement Bakam.
Kungiyar Likitocin Najeriya,NMA ta bakin me magana da yawunta, Dr. Abdulsalam Abdulrazak ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ga manema labarai.
Ya ce kungiyar tasu na mika sakon ta'aziyya ga iyalan Mamacin. Jihar Kaduna na da masu cutar Coronavirus/COVID-19 2,163.