
Hotuna yanda Likitocin dabbobi suka wa Kunkurun da mota ta kade aiki a Sokoto
Likitocin Dabbobi sun yiwa kunkurun da mota ta kade a Jihar Kebbi kuma gadsn bayansa ya karye aiki a Sokoto.
An bayyana cewa shekarun Kunkurun 75 kuma wata Motar Hilux ce ta takeshi akan titi wanda aka kaishi Sokoto dan yi masa aiki.
Kwararrun Likitoci sun taru akansa inda aka samu aka mayar masa da gadan bayanshi da ya karye kuma aka mayar dashi Argungu jihar Kebbi ida dama daga canne aka daukoshi.