
Bidiyo: Yanda ‘yan Bindiga sukawa Me jego da Mahaifiyarta fyade a Kurfi, Jihar Katsina
Dr. Bashir Kurfi wanda shine shugaban kungiyar masu fafutukar Adalci ta Najeriya ya bayar da labarin yanda 'yan Bindiga sukawa wata me jego da mahaifiyarta da ta je kula da ita fyade a Kurfi, Jihar Katsina.
Da yake magana da manema labarai bayan da ya je ziyara garin. Dr. Bashir yace a kullun sai an kashe mutum sannan sai an yiwa mata fyade.
Yace bai dade da dawowa daga Kurfi ba, wata mata ta gaya musu cewa ta je ganin diyarta da ta haihu a garin sai ga 'yan Bindigar sun shiga. Yace sun bata rikon jaririn suka wa diyartata fyade sannan suka baiwa diyar tata jaririn itama suka mata fyaden. Yace wannan abu ne dake faruwa kusan kullun rana ta Allah.