fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Kutse

An yiwa shahararrun mutane irin su Obama, Bill Gates kutse a Twitter

An yiwa shahararrun mutane irin su Obama, Bill Gates kutse a Twitter

Uncategorized
An yi wa shafukan tiwita na manyan mutane da kamfanoni ciki har da Barack Obama da Bill Gates kutse, a wani al'amari wanda ga alama shiryayyen hari ne mafi girma ga dandalin sada zumuntar.   Ɗan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Dimokrat, Joe Biden na cikin mutanen da kutsen ya shafa, da kamfanin Apple da Uber da fitaccen mawaƙi Kanye West da Jeff Bezos. A wani ɓangare na zambar, an wallafa saƙwannin jabu a shafukan mutanen da kutsen ya shafa, inda aka buƙaci mutane su aika gudunmawar dala dubu ɗaya na kuɗin bitcoin, da fatan samun ninkin kuɗinsu.   Asusun bitcoin ya samu kuɗi fiye da dala dubu ɗari zuwa yanzu.   Wani babban editan wata kafar yaɗa labaran harkokin fasaha a intanet, da ake kira CNET, Dan Ackerman ya ce salon damfarar yana kama da na ...