
Allah yawa Sarkin Kuwait Rasuwa
Sarkin Kuwait mai shekara 91, Sheikth Saban al-Ahmed al-Sabah, ya rasu.
Ana saran kaninsa da suke uba daya, Yarima Sheikh Nawaf al-Ahmed, ya maye gurbinsa.
A watan Yuli, aka kai Sheikh Sabah wani asibitin Amurka sakamakon tiyatar da aka yi masa kan wata cuta da ba a bayyana ko mece ce ba Kuwait din.
Tun shekara ta 2006 ya ke mulki a kasar da ke yankin Gulf, kuma ya shafe sama da shekaru 50 ya na sa ido kan harkokinta na ketare.