fbpx
Wednesday, July 15
Shadow

Tag: kwallon kafa

An Gurfanar Da Wani Magidanci Wanda Ya Damfari Yan Kwallo Naira Miliyan 3.5 Akan Cewa Zai Fidda Su Kasashan Waje

An Gurfanar Da Wani Magidanci Wanda Ya Damfari Yan Kwallo Naira Miliyan 3.5 Akan Cewa Zai Fidda Su Kasashan Waje

Wasanni
Ranar Jumma’a, ‘yan sanda suka gurfanar da wani mai shekara 47, Rasheed Salihu, a Kotu na I dake Kubwa a Abuja, kan zargin damfarar mutum biyu naira miliyan 3.6 da nufin zai samo musu biza da kungiyar kwallon kafa a kasar waje. Salihu wanda ke zaune a Bwari cikin Abuja na fuskantar tuhuma ne kan laifukan da suka hada da zamba cikin aminci, saba alkawari, da kuma cuta. Mai karanto laifin, Babajide Olanipekun, ya bayyana wa kotun cewa wadanda suka kawo karar, Asuguo Joseph da Chiwendu Paul sun kai karar lamarin ne Ofishin ‘yan sanda na Byazhin ranar 27 ga watan Yuni. Olanipekun ya ce wanda ake karar ya hada kai da wasu masu daukan ‘yan kwallon kafa ne ya damfari kowannensu miliyan 1.8 tsakanin 2017 da 2020. Ya ce wanda ake karar ya yi musu alkawarin kai su Turai don kwall
Akwai ‘yan Luwadi a kowace kungiyar kwallon kafa>>Tauraron Watford ya bayyana

Akwai ‘yan Luwadi a kowace kungiyar kwallon kafa>>Tauraron Watford ya bayyana

Wasanni
Tauraron dan kwallon kafar kungiyar Watford,  Troy Deeney ya tabbatar da cewa akwai 'yan Luwadi a kowace kungiyar kwallon kafa.   Ya bayana hakane a ganawar da yayi da BBC inda yace amma da yawa suna jin tsoron su fito su bayyana kansu. Yace suna shakkun abinda zai biyo bayane. Yace amma idan aka samu mutum 1 ya fito ya bayyana kansa to zai jawa sauran gora suma su fito su bayyana.   Ya kara da cewa,a yanzu ne daidai lokacin da 'yan kwallon ya kamata su fito su bayyana ainahin bangaren da suke.   Yace yawancin 'yan kwallo da masu motsa jiki sukan yi shakkar fitowa su bayyana cewa su 'yan Luwadine har sai sun gama rayuwar wasansu sun yi ritaya tukuna.
Kwallayen Lewandowski na gasar Bundlesliga sun cika 30 a jiya

Kwallayen Lewandowski na gasar Bundlesliga sun cika 30 a jiya

Wasanni
A jiya sati 6 ga watan yuni Robert Lewandowski yayi nasarar cin kwallon shi ta 30 a gasar Bundlesliga yayin da suka kara da Bayer Leverkusen, kuma Munich sun yi nasara a wasan wanda suka tashi 4-2. Lucas Alario ya tsorata kungiyar Munich yayin daya zira kwallo a minti 10 na farko a wasan, tun daga nan kuma Bayern Munich suka fara yin kokari sosai kuma suka yi nasarar jefa kwallaye guda 3 kafin aje hutun rabin lokaci. Lewandowski yayi nasarar cin kwallon shi ta 30 bayan an dawo daga hutun rabin lokacin, yan wasan Bayern Munich sun yi zanga zangar mutuwar George Floyd yayin da suka sanya wani abun ado na hannu wanda aka rubuta " Rayuwar bakin fata ". George Floyd ya kasance bakar fata kuma ya mutu ne a hannun wani dan sanda a garin Minneapolis dake kasar Amurka.
Mutumin da ya fara bayar da jan kati a gasar kwallon kafa ta duniya

Mutumin da ya fara bayar da jan kati a gasar kwallon kafa ta duniya

Wasanni
Dogan Babacan ne Alkalin wasa na farko dan kasar Turkiyya da ya jagoranci gudanar da wasan karshe a gasar kwallon kafa ta duniya ta FIFA. Babacan ya fara alkalancin wasa a shekarar 1955, inda ya halarci gasar wasanni Olympics ta 1974 da gasar kwallon kafa ta duniya ta FIFA ta 1974. A lokacinda a karon farko a shekarar 1974 aka fara amfani da jan kati, a gasar FIFA ta 1970  babu alkalin wasan da ya bayar da jan katin.     A wasan karshe na gasar kwallon kafa ta duniya ta FIFA ta 1974, an bayar da jan kati a wasan West Germany da Chile. Dogan Babacan ya ba wa dan wasan kasar Chile Carlos Caszely jan kati wanda hakan ya sanya ya shiga tarihi a matsayin alkalin wasa da ya fara bayar da jan kati a gasar ta FIFA. A wannan lokaci akwai Jack Taylor dan kasar Ingila wanda ke taim
Chelsea sun karawa Giroud tsawon kwantirakin shi

Chelsea sun karawa Giroud tsawon kwantirakin shi

Wasanni
Giroud ya kusa barin kungiyar Chelsea yayin da aka bude kasuwar yan wasan kwallon a watan janairu, amma ya fasa saboda Frank Lampard ya kasa samun dan wasan da zai maye gurbin shi. Oliver Giroud ya samu damar shiga tawagar yan wasa 11 na farko a kungiyar Chelsea bayan Tammy Abraham ya samu rauni,kuma Giroud yana kokari sosai kafin a dakatar da wasannin kwallon kafa.   Giroud yana cikin yan wasan da kwantirakin su zai kare a wannan kakar wasan amma yanzu an kara mai zuwa kakar wasan 2020/2021. Shima golan su Willi Cabellero an kara mai shekara daya yayin su kuma Pedro da Willian har yanzu ba'a kara masu ba.   Giroud yace yana jin dadi saboda zai cigana da wasa a kungiyar Chelsea kuma yana so ya ga yasa kayan Chelsea a filin wasan su musamman a gaban masoyam su g...
Yadda wasan Bayern Munich da Union Berlin ya kasance yayin da Munich suka yi nasarar jefa kwallaye biyu

Yadda wasan Bayern Munich da Union Berlin ya kasance yayin da Munich suka yi nasarar jefa kwallaye biyu

Wasanni
Jiya ranar lahadi yan wasan Bayern Munich suka yi tafiya izuwa garin Berlin wanda ke gabacin kasar jamus domin su buga wasa tsakanin su da Union Berlin kuma sun yi nasara a wasan. Kwallayen da Lewandowski da Pavard suka ci sun sa an ba Bayern Munich maki uku, kuma hakan yasa sun wuce abokan hamayyar su wato Dortmund da maki hudu. A lokacin da aka fara buga wasan, Berlin sune suke kokari sosai amma daga baya sai Munich suka kwace masu. Minti shida kafin aje hutun rabin lokaci Subotic ya bugi Goretzaka a kafa kuma rafilin bai nuna wariya ba yayin daya ba Munich penarity, kuma Lewandowski yayi nasarar cin kwallon. Munich sun kara jefa kwallo daya ana gab da gama wasan yayin da Kimmich ya bugo kwana kuma Benjamin Pavard yayi nasarar cin kwallon yayin da golan ya kasa kamata ...
Hotuna da Bidiyo:Kalli yanda wani kwarre ya zana Sadio Mane

Hotuna da Bidiyo:Kalli yanda wani kwarre ya zana Sadio Mane

Wasanni
Wani kwararren me zanene ya zana tauraron dan kwallon kasar Senegal dake bugawa kungiyar Liverpool ta kasar Ingila wasa, watau Sadio Mane.   Salon da yayi amfani dashi wajan yin zanen ya dauki hankulan mutane sosai inda akai ta yaba masa.       https://twitter.com/iam_lordvintage/status/1195787720196530176?s=19 Matasgin dana ya kware wajan iya Zane-zane.
Bidiyo:Kalli abin kayatarwar da ‘yan kwallonnan suka yi a shagon sayayya

Bidiyo:Kalli abin kayatarwar da ‘yan kwallonnan suka yi a shagon sayayya

Wasanni
Wannan wani hoton bidiyon 'yan kwallo ne da ya dauki hankula inda aka gansu sunje sayayyar kaya a wani shagon Supermarket.   Duk abinda suka dauka suna mai irin bugun kwallone wajan sakashi a cikin kwandon sayayya. https://twitter.com/BleacherReport/status/980471478134104064?s=19 https://twitter.com/tvdellosport/status/1259739265451405312?s=19 Abin ya kayatar sosai.
Kungiyar Madrid da Barcelona sun fara yiwa yan wasan su gwajin cutar Covid-19

Kungiyar Madrid da Barcelona sun fara yiwa yan wasan su gwajin cutar Covid-19

Wasanni
Kasar Spain ta kasance daya daga kasashen da cutar Covid-19 tayi kamari kuma a ranar laraba an samu labari cewa gabadaya mutanen da cutar ta kashe sun kai 26,000.     Yan wasan Madrid da Barcelona sun fara yin gwajin cutar coronavirus a ranar laraba yayin da kungiyoyin la liga suke shirin cigana da atisayi saboda suna sa ran cigaba da wasannin su a wata mai zuwa. Kaftin din Barcelona Lionel Messi da dan wasan faransa Antoine Griezmann suna cikin yan wasan da aka yiwa hoto yayin da suke halattar filin atisayin su daya bayan daya a cikin motocin a safiyar ranar laraba, A yan wasan Madrid kuma Eden Hazard  Karim Banzema suna cikin yan wasan da suka halarci gwajin a filin atisayin su. Ana sanar da sakamakon gwajin cutar ne cikin awanni 48, kuma gwajin yana daya d