Sunday, June 7
Shadow

Tag: kwallon kafa

Unai Emery ya bayyana sunan dan wasan da zai maye gurbin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi

Unai Emery ya bayyana sunan dan wasan da zai maye gurbin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi

Wasanni
Tsohon shugaban Arsenal da PSG Unai Emery ya bayyana sunan tauraron da zai maye gurbin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a matsayin zakaran wasannin kwallon kafa na duniya. Messi da Ronaldo sun mamaye duniyar wasan kwallon kafa fiye da shekaru goma da suka gabata kuma sun lashe kyaututtukan balloon d'Or har sau 11 tsakanin su. Amma yanzu zakarun sun fara fuskantar shekaru su na karshe a wasannin kwallon kafa yayin da shi kuma Emery ya bayyana dan wasan daya horar a kungiyar PSG a matsayin zakaran da zai maye gurbin Ronaldo da Messi. Kuma dan wasan shine tauraron Brazil wato Neymar, wanda yayi aiki tare da Emery a kungiyar Paris saint German bayan sun siyo shi daga Barcelona a farashin da ba'a taba siyan wani dan wasa ba, euros miliyan 198 a shekara ta 2017. Emery ya gaya...
An gayawa tauraron Barcelona Messi cewa cin kwallaye daya keyi ba baiwa bane

An gayawa tauraron Barcelona Messi cewa cin kwallaye daya keyi ba baiwa bane

Wasanni
Tim Sherwood yace nasarorin da Lionel Messi ya samu a wasannin kwallon kafa ba baiwa bace naci ne da kuma kokarin da yake yi yasa ya same su, kuma tsohon manajan Tottenham din yace kwallayen da tauraron barcelonan yake ci ba baiwa bace.   Mutane dayawa suna tunanin cewa Messi shine zakaran wasan kwallon kafa na duniya kuma yaci kwallaye guda 627 a wasanni guda 718 daya buga a rayuwar shi. Dan wasan Argentina ya kafa tarihi a gasar la liga saboda yawanci yana cin kwallo a kowane wasa yayin da yayi nasarar cin kwallaye guda 438 a wasanni guda 474 na la liga. Duk da haka dai Sherwood yace wannan abun ba zai taba zama baiwa ba kuma shi ya yarda cewa nasarorin Messi saboda kokari ya same su. Ya gayawa DailyMail cewa shi bai yarda cewa akwai wani dan wasan mai baiwa ba k...
Kayatattun hotuna:Kalli Ronaldo da ‘ya’yansa suna Shakatawa

Kayatattun hotuna:Kalli Ronaldo da ‘ya’yansa suna Shakatawa

Wasanni
Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo kenan a wadannan kayatattun hotunan da ya dauka tare da 'ya'yansa yayin da suke shakatawa a tsibirin Madeira inda suke zaune. https://www.instagram.com/p/B_rtD6GAigC/?igshid=1hmdcwg7of70r   https://www.instagram.com/p/B_kngAbAfu0/?igshid=167qk795e2p5d Tun dai da aka fara fama da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19, Cristiano Ronaldo ya killa e kansa da iyalansa a Tsibirin dake kasar ta haihuwa watau Sifaniya.
Ighalo yayi jawabi gami da yan wasa United guda biyu Greenwood da Paul Pogba

Ighalo yayi jawabi gami da yan wasa United guda biyu Greenwood da Paul Pogba

Wasanni
Odion ighalo ya ambata cewa abokin aikin shi Mason Greenwood zai zamo babban dan wasan Manchester United nan da shekaru biyu ko uku.   Greenwood yana jin dadin kasancewar shi a kungiyar United yayin da saurayin yayi nasarar jefa kwallaye har guda 12 a wannan kakar wasan. Duk da kokarin da Greenwood da abokin aikin shi  Marcus Rashford suke yi, United sai da suka kara kawo wani dan wasa gaba a watan janairu. Manchester sun dogara ga yan wasan su dake tasowa bayan sun kasa maye gurbin Romelu Lukaku a kakar wasan bara. Dan wasan da kawo siyo shine Ighalo wanda suka aro daga kulob din Sin na Shanghai Shenhua har izuwa karshen wannan kakar wasan. Kuma dan wasan najeriyan bai basu kunya ba yayin da yayi nasarar jefa kwallaye har guda 4 a wasanni guda uku daya fara bugawa a
Sakamakon taron premier lig yayin da manajan Leicester  City  ke cewa Liverpool sun cancanci kofin

Sakamakon taron premier lig yayin da manajan Leicester City ke cewa Liverpool sun cancanci kofin

Wasanni
Premier lig sun bayyana cewa babu wata shawara da suka yanke a taron da suka gudanar a yau, kawai sai dai kungiyoyin sun kara tabbatar da cewa suna so a gama buga wannan kakar wasan tare da bin dokoki kuma sun jinjinawa gwamnati gami da goyon bayan da suke basu. An samu labari daga The Times cewa gwamnati ta bayar da shawara cewa ba kowane wasa za'a sanar da jama'a saboda ana tunanin cewa mutane zasu iya taruwa a wajen filin wasan.     Magajin garin Liverpool yace jama'a zasu iya taruwa a wajen filin wasan Liverpool wato Anfield suyi biki idan aka baiwa liverpool kofin premier lig. Manajan leicester city Bredan Rodgers yace Liverpool itace babbar kungiyar a yanzu saboda suna kokari sosai kuma sune a sama teburin gasar premier lig da maki 25 saboda haka abun k...
Bosnich yace ya kamata United su gaggauta siyan kwararren dan wasa maimakon Ighalo

Bosnich yace ya kamata United su gaggauta siyan kwararren dan wasa maimakon Ighalo

Wasanni
Tsohon golan Manchester United Mark Bosnich yace United suna bukatar siyan kwararren dan wasan da zai maye masu gurbin Marcus Rashford.     Rashford yana kokari sosai a wannan kakar wasan kuma ya kasance dan wasan da yafi sauran yan kungiyar jefa kwallaye cikin raga yayin da yayi nasarar cin kwallaye har guda 14. Amma sai dai ya samu karaya a bayan shi a watan janairu kuma hakan ne yasa United suka aro tsohon dan wasan gaba na Watford Odion ighalo daga kungiyar Shanghai Shenhua. Ighalo ya burge sosai a kungiyar yayin da yayi nasarar cin kwallaye 4 a wasannin guda takwas daya kuma hana ne yasa ole gunnar yake tunanin yi mai sabon kwantirakin a kungiyar. Bosnich yayi wasa a kungiyar Manchester United har na tsawon shekaru 2 kuma yace ighalo yana burge shi amma ...
Braithwaite yace zai kasance daya daga cikin zakarun la liga da suka fi jefa kwallaye cikin raga kuma babu wanda yake motsa jiki kamar yadda yake yi

Braithwaite yace zai kasance daya daga cikin zakarun la liga da suka fi jefa kwallaye cikin raga kuma babu wanda yake motsa jiki kamar yadda yake yi

Wasanni
Tsohon dan wasan gaba na leganes, Bordeaux da Middlesbrough ya bayyana cewa zai Kara da manyan yan wasan kungiyar Barcelona kuma zai kasance daya daga cikin zakarun la liga da suka fi sauran yan wasan gasar jefa kwallaye cikin raga. Braithwaite yaci kwallaye guda 10 a shekara daya da rabi da yayi a kungiyar leganes sai kuma kwallaye 4 daya ci a kungiyar Bordeaux sannan yaci kwallaye guda 8 a wasanni guda 36 daya buga a kungiyar Middlesbrough. Barcelona sun siyo dan wasan ne daga kungiyar leganes a farashin euros miliyan 15 domin ya maye masu gurbin yan wasan su da suke fama da raunika luiz Suarez da Dembele. Braithwaite yace yanzu ana cikin hutu kuma wannan babbar dama ce a gurin shi saboda ya san ba wani dan wasan da yake motsa jiki kamar yadda yake yi. Braithwaite...
Wasu mayan manajonin kwallon kafa sun fifita Messi akan Ronaldo

Wasu mayan manajonin kwallon kafa sun fifita Messi akan Ronaldo

Wasanni
Messi da abokin hamayyar shi Cristiano Ronaldo sun mamaye duniyar wasan kwallon kafa sama da shekaru goma kuma sun samu kyaututtuka da dama a wasannin kwallon kafan. Messi yayi nasarar lashe kyautar balloon d'Or har sau shida yayin da shi kuma Cristiano Ronaldo ya ci kyautar balloon d'Or din sau biyar amma sai dai Messi bai taba samun wata kyauta ba a kasar shi ta Argentina, shi kuma Ronaldo ya samu kyaututtuka har guda biyu a kasar shi ta Portugal, kuma Ronaldo ya lashe gasar champions lig har sau biyar yayin da shi kuma Messi yaci gasar sau hudu. Mutane da dama suna yin musu akan Messi da Ronaldo hadda masu yin sharhin wasanni ma suna yin muhawara gami da yan wasa, yanzu haka wasu daga cikin manajonin kungiyoyin wasan kwallon kafa sun bayyana ra'ayin su akan yan wasan kamar...
Mahaifin Aubameyang ya bukaci yaran nashi da ya ci gaba da wasa a kungiyar Arsenal

Mahaifin Aubameyang ya bukaci yaran nashi da ya ci gaba da wasa a kungiyar Arsenal

Wasanni
Mahaifin Pierre Emerick Aubameyang wato Pierre Francois ya saka wani sabon hoto a shafin shi na Instagram wanda asalin hoton yake nuna lokacin da Arsenal suke yima yaran nashi kwantiraki a shekara ta 2018 bayan sun siye shi daga kungiyar Borussia Dortmund. Pierre Francois yayi wani rubutu a jikin hoton yayin da yake cewa "kasan abun da zaka yi dan uwa". Wannan rubutun da yayi yana nuna cewa yana so yaran nashi ya cigaba da wasa a arewacin landan. Aubameyang yana kokari sosai a kungiyar yayin da yayi nasarar jefa kwallaye har guda 49 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 10 a wasanni guda 75 daya buga na premier lig. An samu labari daga Mirror cewa kwantirakin Aubameyang zai kare ne nan da kakar wasan badi kuma har yanzu basu sasanta da dan wasan ba gami da sabon kwanti...
Chelsea zasu rasa Christian Pulisic in har suka siya Philippe Coutinho

Chelsea zasu rasa Christian Pulisic in har suka siya Philippe Coutinho

Wasanni
An shawarci kungiyar Chelsea cewa ba sai sun siya Coutinho ba a wannan kakar wasan saboda suna da dan wasan dake buga masu lamba 10. Daya daga cikin masu sharhi na ESPN Don Hutchison yace Chelsea zasu rasa Christian Pulisic in har suka siya dan wasan Brazil din. Chelsea suna samun nasara wurin siyan dan wasan Brazil din yayin da Bayern Munich suka fasa siyan shi bayan sun aro shi daga kungiyar Barcelona. Barcelona suna kokarin siyar da dan wasan domin su samar ma Neymar da Lautaro Martinez matsugunni a kungiyar duk da cewa bai zama lallai su siya gabadaya yan wasan ba. Hutchison yana gargadin Chelsea gami da siyan Philippe coutinho da suke so suyi saboda zasu rasa Christian Pulisic. Dan wasan amurikan Pulisic ya shiga kungiyar Chelsea ne a kakar wasan bara a farashin e...